Wa da wane ne suka halarci bikin Messi?

Messi and Antonelo Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Messi ya gamu da rabin-ran tasa ce tun yana ɗan shekara biyar da haihuwa

Tauraron ɗan ƙwallon ƙafar Argentina, Lionel Messi ya angwance da rabin ransa tun lokacin yarinta, Antonela Roccuzzo a wani biki da aka yi a mahaifarsa ta Rosario.

Wasu daga cikin gaggan 'yan ƙwallon duniya, ciki har da abokan buga ƙwallon Messi a Barcelona kamar Luis Suarez da Neymar sun halarci bikin a wani otel ɗin alfarma.

Messi mai shekara 30 da Antonela Roccuzzo 'yar shekara 29 sun haifi ɗa biyu tare.

Fitattun 'yan ƙwallon ƙafa da mashahuran mutane na daga cikin baƙi guda 260, da kuma ɗaruruwan 'yan sanda da aka jibge don wannan gagarumin biki.

Ango da amaryar sun gamu ne tun kafin Messi ya shiga Barcelona yana ɗan shekara 13, a ƙoƙarinsa na kama sana'ar take leda ka'in da na'in.

Jaridar Clarin ta Argentina ta bayyana bikin a matsayin "auren shekara" da kuma "auren ƙarni".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsoffin abokan buga ƙwallon Messi da dama, ciki har da Xabi Alonso da Cesc Fàbregas da Carles Puyol sun halarci bikin tare da abokan zamansu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gerard Piqué (hagu) da matarsa Shakira sun ɗauki hoto da ma'aikatan filin jirgin sama lokacin da suka sauka Rosario

Magoya baya daga maƙwabtan yankuna sun je birnin Rosario mai nisan kilomita 300 daga Buenos Aires babban birnin Argentina don ganin wasu mashahuran baƙi da suka hada da taurarin ƙwallon ƙafa Fabregas da Di Maria da Pique da matarsa, Shakira, fitacciyar mawaƙiya 'yar ƙasar Colombia.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cincirindon magoya baya ne suka taru a wajen otel ɗin da aka sha biki

Labarai masu alaka