Chelsea za ta sayi Rudiger da Bakayoko da kuma Sandro

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kociyan Chlesea, Antonio Conte yana sayan 'yan wasan da za su taimaka wa kungiyarsa a kaka na gaba

Chelsea tana kokarin kammala yarjejeniyoyi uku kan kudi fam miliyan 125 na sayan dan wasan Monaco Tiemoue Bakayoko da dan wasan Roma Antonio Rudiger da kuma dan wasan Juventus Alex Sandro, wanda ka iya kafa tarihi a amsatyin wanda kulob din ya fara saya kan kudi fam miliyan 60, in ji Daily Telegraph.

Ita kuma jaridar Sun ta ruwaito cewar Chlesea tana tunanin sayan dan wasan Porto Alex Telles maimakon Sandro, wanda kungiyar Paris St-Germain ma take hako.