Dan Nigeria ne ya kai hari asibitin Amurka?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Yan sandan ko-ta-kwana sun shiga asibitin

Wani dan bindiga ya bude wuta a cikin wani asibiti da ke anguwar Bronx na birnin New York, inda ya kashe wata likita ya kuma jikkata mutum shida, biyar daga cikinsu sun ji ciwo sosai.

Dan bindigan, wanda tsohon likita ne a asibitin, ya kashe kansa a harin.

Magajin gari Bill de Blasio ya ce harbin ba aikin ta'addanci ba ne, amman lamari mai alaka da wajen aiki ne.

Ya ce likitar da maharin ya kashe mace ce, yana mai karawa da cewar ana kokarin ceton rayukan wadanda suka jikkata a harin.

Image caption 'Yan sanda sun tabbar da cewar wannan hoton da aka samu daga shafin Facebook na Henry Bello ne

Tun kafin a bayyana sunan maharin a hukumance ne wasu 'yan sanda suka bayyana wa kafafan yada labaran Amurka cewar sunan maharin ne Henry Bello, mai shekara 45, wanda ya taba aiki a asibitin.

Gidan talabijin din NBC ya ambato majiyoyi suna cewa Mista Bello ya bar aiki a asibitin a shekarar 2015.

Kwamishinan 'yan sanda James O'Neill ya ce mutumin ya nemi ya cinna wa kansa wuta kuma ya mutu ne sakamakon raunin da ya ji wa kansa.

Bayanai a shafukan sada zumunta sun ce likitoci da masu aikin jinya sun rufe kansu cikin ginin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan birnin New York police sun yi kira ga mutane su guji zuwa kusa da sibitin

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewar wasu 'yan Najeriya da 'yan sanda a birnin na New York sun tabbatar masa da cewar mutumin, Henry Michael Bello, dan asalin Najeriya ne.

Kamfnin dillancin labaran Najeriyar ya ce Bello ya fara aiki da sibitin ne a watan Augustan shekarar 2014 kuma an taba kama shi a baya kan laifukan da suka hada cin zarafi ta lalata da wuce kofar karfe ba bisa ka'ida ba da fitsari a fili da kuma sata.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Likitoci na cikin wadanda suka ji ciwo

Wani majinyaci a sashin da ake daukar hoton sassan jiki, Felix Puno, ya wallafa wani sako a shafibsa na Twitter cewar: "Ginin yana a garkame. Ana kan daukar hoton jiki na ne jami'an tsaro suka sanar da mu cewar wani yana harbi."

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mayor Bill de Blasio ya ce harbin wani kebabben abu ne kuma da alaman cewar abu ne wanda ya shfi wajen aiki.

Karin bayani