Nigeria: 'Wutar lantarki ce silar gobarar sakatariyar tarayya'

Nigeria's Federal Secretariat Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sakatariyar gwamnatin tarayyar Najeriya da ke Abuja na da ma'aikatun gwanati da yawa a cikinta

Jami'ai a Najeriya sun ce gobarar da ta tashi a bangaren ma'aikatar kiwon lafiya na ginin sakatariyar gwamnatin tarayyar kasar dake Abuja ta auku ne sakamakon matsalar wutar lantarki.

A ranar Asabar ce gobarar ta tashi, wacce jami'ai suka ce ba ta yi muni sosai ba.

A wata sanarwa, Darakatar yada labarai ta ma'aikatar lafiyar, Boade Akinola, ta ce gobarar ba ta haddasa wata asarar azo-a-gani ba.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ambato Daraktan ayyuka a ma'aikatar lafiyar, Mista Felix Ogenyi, yana cewa wutar ba ta kona fayel ko daya ba kuma ba ta kashe kowa ba.