An yi zanga-zangar kin jinin gwamnati a London

London March Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga zangar sun bukaci Firayiministar Burtaniya Theresa May ta yi murabus.

Dubban masu zanga-zanga sun yi maci a wasu manyan titunan tsakiyar London domin nuna rashin jin dadin su da irin manufofin tattalin arziki na gwamnatin Burtaniya.

Masu zanga-zangar sun yi kiran a kawo karshen matakin tsuke bakin aljihu na gwamnatin kasar karkashin jam'iyyar Conservative, sannan sun bukaci Firayiministar Burtaniyar, Theresa May ta yi murabus.

Kungiyoyin ma'aikata ne suka shirya zanga-zangar, kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Labour, Jeremy Corbyn, ya na daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai ga dandazon mutanen.

Jam'iyyar Conservative ta rasa babban rinjayenta a majalisar dokokin kasar a zaben watan jiya, yayin da ita kuma jam'iyyar adawa ta Labour ta kara yawan kujeru, sai dai duk da hakan, tana bayan jam'iyyar ta Conservatives.