Jaririn da aka harba da bindiga a cikin mahaifa bai mutu ba

Brazil baby Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyoyin masu hada-hadar miyagun kwayoyi ne suka yi harbe-harben a birnin Duque de Caxias.

Wani jariri, sabon haihuwa, yana cikin mawuyacin hali a Brazil, bayan wasu harsasai biyu, da aka yi harbin kan mai uwa da wabi da su, sun same shi lokacin da yake cikin mahaifa.

Mahaifiyarshi, wacce cikin nata ke wata tara, an yi mata tiyata, inda aka ciro jaririn domin a ceci rayuwar shi.

'Yan sanda sun ce wasu kungiyoyin masu hada-hadar miyagun kwayoyi ne suka yi harbe-harben a birnin Duque de Caxias.

Harsasan biyu sun ratsa ta kashin kwankwason mahaifiyar jaririn ne, inda suka raunata jinjirin a kirjinsa da kuma kunnensa daya.

Mahaifiyar jaririn tana asibiti itama, amma ance jikin nata da sauki.

Ana ci gaba da samun karuwar tashe-tashen hankali a birnin Rio de Janeiro, da wasu biranen Brazil din da dama, wadanda suke fuskantar matsalar kudi yayin da tattalin arzikin kasar ya yi tabarbarewa mafi muni a tarihinta.