'Rashin fita zaɓe na kassara shugabanci nagari'

Voters in Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akasari zaɓen ƙananan hukumomi a Nijeriya bai cika armashi ba, don kuwa kusan duk jam'iyya mai mulki a jiha ce ke cinye mafi yawan kujerun shugabanni da kansilolin ƙananan hukumomi.

Yawan fitar jama'a ƙwansu da kwarkwatarsu su kaɗa ƙuri'u a lokacin zaɓuka, ka iya yin tasiri wajen tausasa gwiwar 'yan siyasa su wanzar da shugabanci nagari.

Jami'in wata ƙungiya mai sa ido kan zaɓuka, Assembly For Peace ne ya yi wannan ankaraswa jim kaɗan bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya.

Mallam Yakubu Hussaini Muhammad Takai ya ce: "da mutane sun yi tururuwa wajen zaɓar shugabanninsu, mutum ya ga ana kokawar zaɓarsa, to wannan zai sa masa tausayi a cikin ransa."

"Shugaba zai ji yadda mutane suka yi tururuwar nan, dole in fito musu da ayyuka(n raya ƙasa) iri daban-daban na yi musu," in ji shi.

A cewarsa wannan matsala ce ga al'ummar Nijeriya gaba ɗaya, "kuma yana kashe gwiwar su kansu 'yan siyasa, su kasa yi wa mutane abin da ya kamata."

Ya ce mutanen gari ba su ba da haɗin kai ba a zaɓen ƙananan hukumomin jihar Jigawa.

"Duk inda ka je za ka ga cewa akwai 'yan matsaloli na fitar mutane (rumfunan zaɓe) gaskiya."

Sai dai wasu 'yan Jigawa a unguwar Jigawar Tsada sun faɗa wa BBC a lokacin da zaɓen ke gudana ranar Asabar cewa zaɓen da rashin yinsa duk ɗaya ne.

Wani Adamu Ibrahim Jigawar Tsada ya ce shi jam'iyyarsa ta PDP ta yanke shawara janyewa daga zaɓen don haka bai ga hujjar zuwa cibiyar kaɗa ƙuri'a ba.

Shi ma wani Isah Danjuma ya ce: "Ban je ba gaskiya. Ko da ka je ka yi zaɓen aikin banza ne."

'Yan Nijeriya da dama ne kan yi ƙorafi cewa abin da suke zaɓa a lokacin zaɓukan ƙananan hukumomin ƙasar, akasari ba shi ake ba su ba.

Wakilin BBC Ibrahim Isah ya ruwaito cewa wannan dai ba shi ne karon farko da jam'iyya mai mulki ta yi kusan cinye duk a zaɓen na jihar Jigawa ba.

Sai dai wani wakilin jam'iyyar APC a zaɓen ƙananan hukumomin Jigawa, Shitu Jigawar Tsada ya ce sun shaida fitar ɗumbin mutane a zaɓen.