Terry Gobanga: 'Yadda gungun maza suka min fyade ranar bikina'

Terry Gobanga Hakkin mallakar hoto Josse Josse

Lokacin da aka ji shuru ba a ga isowar amaryar Terry Gobanga ba, babu wanda ya kawo a ransa cewa sace ta aka yi, kuma har ma an jefar da ita a gefen hanya bayan an yi mata fyade.

Kodayake amaryar ta tsira da ranta, wannan ne abin da ya faru da matashiyar malamar cocin wadda take zaune a birnin Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

An shirya kasaitaccen biki ne. Ni malamar coci ce, don haka 'yan cocinmu da kuma 'yan uwana duka sun tabbatar mini da cewa za su halarci bikina.

Angona Harry da ni kaina muna cikin farin cikin sosai don fatan ganin wannan rana - wadda za a daura mana aure a cocin All Saints Cathedral da ke birnin Nairobi.

Sai dai a daren jajiberin ranar na fahimci cewa akwai wasu daga cikin kayan da angona zai sa a ranar a wurina.

Harry ba shi da wasu kayan da zai sanya a ranar bikinmu bayan na wurina. Saboda haka wata kawata da ta zo wurina ta bukaci na ba ta kayan don ta kai mai su da sassafe washegari.

Muka tashi da asuba tare da ita, kuma na raka ta tashar shiga mota.

A kan hanyata ta komawa gida na wuce wani mutum zaune a kan gaban wata mota - daga nan ne sai na ji ya cafkoni daga baya kuma ya jefa ni bayan motar. Akwai wasu mutum biyu da suke cikin motar.

Sai suka fara gudu da motar. A ganina abin duka ya faru ne cikin kiftawar ido.

Mutanen suka cusa mini tsumma a bakina. Ina ta shure-shure da doke-doke da kuma kokarin yin kururuwa. Na yi nasarar cire tsumman da aka sanya mini a baki, sai na yi ihu na ce: "Yau ce fa ranar aurena'!" Wannan ne lokacin da na fara shan naushin farko. Guda daga cikinsu ya ce min "ki ba da hadin kai, ko ki mutu".

Hakkin mallakar hoto Terry Gobanga

Yayin da mutanen suke min fyade na sadakar mutuwa zan yi, amma ina ta kokarin kwatar raina saboda haka yayin da daya daga cikinsu ya cire tsumman da aka sa min a baki, sai na sa baki na ciji mazakutarsa.

Jin zabin abin da na yi masa, sai ya fasa ihu kuma sai wani ya caka mini wuka a cikina. Daga nan ne sai suka bude kofar motar da ke ci gaba da gudu, aka kuma wurgo ni waje.

An jefar da ni ne a wani wuri mai nisa daga unguwarmu a Nairobi. Fiye da sa'o'i shida ke nan da faruwar al'amarin.

Wata yarinya ta ga lokacin da aka jefar da ni daga motar, sai ta kira kakarta. Mutane suka taru a kaina. Yayin da 'yan sanda suka iso wurin sun zaci cewa na mutu.

Sai suka lullube ni, suka kama hanyar mutuware da ni. Amma a kan hanyar ne sai na yi tari. Daga nan sai dan-sandan ya ce: " Tana da rai fa". Kuma sai ya juya da motar zuwa babban asibitin gwamnati da ke Kenya.

An kai ni asibitin ne ban san halin da nake ciki ba. Cikin jini kusan tsira-tsira nake kuma fuskata a kumbure bayan naushin da na sha.

Ban san abin da daya daga cikin ma'aikatan jinyan asibitin ta gani a jikina ba kafin ta fara zaton cewa ni amarya ce.

Sai ta cewa sauran ma'aikatan "ku je ku bincika coci-coci da ke kusa ko akwai wata amarya da ta bata".

Bisa arashi, cocin farko da suka fara kira ita ce All Saints Cathedral. "Akwai wata amarya da ta bace daga cocin nan?" in ji wata nas.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cocin All Saint Cathedral ita ce tsohuwar cocin darikar Anglican a Nairobi

Limamin cocin ya ce: "Eh, akwai wani daurin aure da za a yi da misalin karfe 10 amma amaryar ake jira don ba ta iso ba har yanzu."

Yayin da ba a ganni a cocin ba, sai iyayena suka fara nuna damuwa. Aka tura mutane suka bazama nema na. Daga nan sai jita-jita ta bazu. Wasu suka rika cewa "ko ta sauya ra'ayi ne?" Wasu kuma suka "A'a da wuya ta yi hakan, to me ya faru."

Bayan wani dan lokaci, sai aka bukaci wadanda suka halarci bikinmu da su matsa gefe don a karbi wani biki da aka shirya yi bayan na mu. Harry kuma aka ce ya je wani daki don ya zauna ya jira.

Yayin da suka samu labarin wurin da nake, sai iyayena suka iso asibitin tare da wasu daga cikin mahalarta bikin. Harry yana dauke da rigar da zan sanya a ranar. Hatta 'yan jarida su suma sun samu labarin abin da yake faruwa.

An sauya mini asibiti don na samu sukuni. A can ne sai likitoci suka dinke wurin da aka caka mini wuka kuma suka shaida mini wani mummunar labari: "Raunin da kika ji a ciki ya yi zurfi sosai har ya taba mahaifarki kuma ba za ki iya haihuwa ba ke nan."

Hakkin mallakar hoto Terry Gobanga

Daga nan sai aka ba ni magunguna ciki har da wanda zai kare ni daga kamuwa da cutar kanjamau ko SIDA. Hankalina ya tashi na kasa gasgata abin da ke faruwa da ni.

Harry ya ci gaba da shaida mini cewa zan aure ki. "Ina so na kula da ke, zan tabbatar da cewa kin dawo hayyacinki a hannuna a gidana," in ji shi.

Batun gaskiya ba na cikin halin da zan iya cewa Eh ko kuma A'a saboda yadda raina yake gannin mutanen nan uku a kodayaushe da kuma abin da ya faru.

Bayan wasu kwanaki da na fara dawowa hayyacina, na kalle shi na rika neman gafarsa. Ji nake kamar na ba shi kunya.

Don akwai mutanen da ke cewa ai laifina ne da na bar gida da asuba. Abin akwai cin rai, amma Harry da 'yan uwana sun ba ni kwarin gwiwa.

'Yan sanda ba su yi nasarar kama wadanda suka yi mini fyaden ba. A duk lokacin da suka kama wasu miyagu sukan gayyace ni da na je na duba fuskokinsu watakila ko su ne. Amma ni hakan yana kara dawo min da bakin cikin kawai a raina. Don haka a karshe sai ce musu: "Ni na hakura, a bar batun kawai."

Bayan wata uku an shaida mini cewa ba na dauke da cutar kanjamau kuma na ji dadin wannan labarin, sai dai an ce na kara jira har tsawon wata uku kafin a iya tabbatar da hakan gaba daya. Lokacin ne Harry da ni muka fara shirin kara yin aure.

Kodayake ban ji dadin yadda 'yan jarida suka yi min kutse ba, wata mata wadda ta karanta labarina a jarida ta bukaci za ta gana da ni. Sunanta Vip Ogolla kuma ita ma an taba yi mata fyade. Muka yi magana kuma ta ce mini ita da kawayanta za su dauki nauyin duk abin da za a yi a bikinmu. "Duk abin da kike so shi ne za a yi," in ji ta.

Hakan na rika yi musu lissafin abubuwan da muke bukata a ranar. A da ina tunanin daukar hayar rigar da zan sanya a ranar ne, amma yanzu zan samu wadda za ta zama mallakina.

A watan Yulin shekarar 2005, bayan wata bakwai da shirya bikinmu na farko, sai aka daura mini aure da Harry. Daga nan ne muka fara cin amarci.

Hakkin mallakar hoto Terry Gobanga
Image caption An daura auren Harry Olwande da Terry ne a watan Yulin shekarar 2005

Bayan kimanin wata guda, ina tare da Harry a gida da daddare gari ya yi sanyi sosai. Sai ya shigo da wuta daki don mu ji dumi. Bayan mun kammala cin abincin dare sai ya fitar da ita. Daga nan sai ya ce mini yana ganin jiri bari ya je ya kwanta, a lokacin ban yi tunanin cewa wani abu ba ne babba.

Ni ma sai jikina ya rikice amma kuma jikin mijina sai ya kara tabarbarewa yake har abin ya kai shi ga suma. Sai na yi ta maza na dauki waya na sanarwa da wata makwabciyarmu abin da ke faruwa.

Na san lokacin da ta shigo gidanmu amma daga nan kawai sai na ganni a kan gadon asibiti.

Sai na tambayi wurin da mai gidana yake . Aka ce yana wani daki ana duba shi. Sai na ce: "Ni malamar coci ce na san yadda abubuwa suke tafiya a rayuwa, ina so a bayyana min gaskiyar abin da ke faruwa." Sai likitan ya dube ni ya ce: "Ki yi hakuri mijinki ya mutu."

Gani nake kamar ba da gaske yake ba.

Hakkin mallakar hoto Terry Gobanga
Image caption Terry tana sa wa Harry zobe a yatsansa

Komawa coci don yin jana'izar mijina wani abin bakin ciki ne kwarai da gaske. Wata daya da ya wuce muna cikin farin ciki tare da Harry yana gabana ina murmushi. Yanzu muna tare da shi a nan amma shi yana kwance a cikin akwatin gawa ne a wannan lokacin.

Wasu mutane suna ganin ni ce nake da farar kafa don haka suka hana 'ya'yansu karasowa kusa da ni. "Akwai wani abu mummuna da yake tattare da ita," in ji su.

Akwai lokacin da ni da kaina nake ganin kamar akwai kamshin gaskiya a maganarsu.

Har ila yau akwai masu zargina da kisan mijina. Wannan shi ya fi ci min rai - ina shiga damuwa sosai. idan na tuna da hakan.

Sai dai binciken da aka gudanar kan abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mijina ya gano cewa gurbatacciyar iskar Carbon Monoxide ce ta cika dakinmu, wanda hakan ya jawo karancin iskar da ake shaka don numfashi a lokacin.

Na karaya sosai ta fuskar imanina da Ubangiji, na kasa ci gaba da rayuwa kamar kowa.

Wata rana ina zaune sai na ga wasu tsuntsaye suna wasa sai na ce: "Ubangiji, ya ya za ka kula da tsuntsaye amma ka ki kulawa da ni?" A wannan lokacin ne na fahimci cewa akwai sa'a 24 a kowace rana da nake batawa wajen tunani. Kafin ka ce wani abu sai na ankara da cewa na bata mako guda, wata guda kai har ta kai ni da bata shekara guda a cikin wannan hali. Abin yana da wuyar fahimta.

Na shaida wa kowa cewa ba zan kara yin wani auren ba. Ubangiji ne Ya karbi mijina kuma ba na so na sake shiga irin wannan halin kuma. Hali ne da ba zan yi fatan wani ma shiga ba. Tashin hankalin yana da yawa, ina jin shi har cikin yatsuna.

An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi fyade

Basarake ya yi wa yarinya 'fyade' a Katsina

Turkiyya ta janye dokar yin afuwa kan fyade

Amma akwai wani mutum, mai suna Tonny Gobanga, wanda ya rika kawo mini ziyara. Ya rika karfafa mini gwiwa yana cewa na rika tunawa da mijina. Wani lokaci da ya yi kwana uku bai kirani a waya ba sai na fara fushi. A wannan lokacin ne na fahimci cewa kaunarsa ta kama ni.

Hakkin mallakar hoto Terry Gobanga
Image caption Tonny da Terry Gobanga

Tonny ya bukaci ya aure ni amma sai na ce ya je ya sayi mujalla don ya karanta labarina watakila zai iya sauya ra'ayinsa a kaina. Bayan da ya yi abin da na umarce shi, sai ya dawo wurina ya ce da ni shi dai zai aure ni haka.

Amma sai na ce: "Akwai wani abu - Ba zan iya haihuwa ba, don haka ba zan aure ka ba."

"Haihuwa kyauta ce daga Allah," in ji shi. "Idan mun same su Alhamdulillah. Idan kuma ba su samu ba, to kin ga zan kara samun isashen lokacin kulawa da ke, ke nan."

Kalamansa suka ratsa jikina don haka sai na ce na amince.

Tonny ya je gida ya sanar da iyayensa wadanda suka bayyana farin cikinsu gabanin su ji labarina.

"Ba za ka aure ta ba - wannan tsinanniyar," in ji su. Mahaifin mijina ya ki zuwa daurin aurenmu, amma duk da haka ba a fasa daura mana auren ba.

Kimanin mutum 800 ne suka halarci bikinmu, kodayake na san cewa wasu sun yi hakan ne don kawai su kashe kwarkwatar idanunsu.

Shekara uku ke nan bayan aurena na farko, a tsorace nake. Yayin da ake daura mana auren na yi ta kuka ina cewa: "Allah ga ni gareka, kada ka bari ya mutu." Jama'ar da suka zo su ma suka rika taya mu da addu'a.

Shekara daya bayan auren sai na fara rashin lafiya, na nufi wurin likita - abin mamaki sai ya shaida mini cewa ina dauke da juna biyu ne.

Da lokacin haihuwata ya yi sai na haifi diya mace wadda muka sa wa suna Tehille. Shekara hudu bayan nan, muka kara samun diyarmu ta biyu ita kuma muka rada mata suna Towdah.

Hakkin mallakar hoto TERRY GOBANGA

A yanzu muna dasawa da surukina sosai.

Na rubuta wani littafi mai suna, Crawling out of Darkness, ya kunshi duka abin da ya faru da ni.

Har ila yau na kafa wata gidauniya mai suna Kara Olmurani, wadda take taimakon wadanda suka tsira daga fyade kamar yadda nake kiransu - ba wadanda aka wa fyade ba kamar yadda galibin mutane ke cewa.

Muna kokarin samar musu da wani gida da za su rika zama don su murmure daga abin da ya faru da su kafin su sake dawo cikin al'umma.

Na yafe wa wadanda suka min fyade. Ba abu ba ne mai sauki amma na fahimci cewa kada ka damu da wadanda ba su da kulawa.

Hakazalika addinina yana son yafiya - ba ya so a rama sharri da sharri, sai dai da alheri.

Labarai masu alaka