Trump: 'Ni shugaban kasa ne mai tafiya da zamani'

Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump ya ce shafinsa na Twiiter ya taimake shi wajen lashe zaben Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya kare kansa kan yadda yake yawan amfani da kafofin sada zumunta musamman shafin Twitter.

Ya yi hakan ne bayan wasu kalamai da ya yi game da wasu ma'aikatan kafar yada labarai ta MSNBC da ke Amurka.

"Ina yawan amfani da kafar sada zumunta ne saboda ni shugaban kasa ne mai tafiya da zamani," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

'Yan jarida ba sa fadar gaskiya — Trump

Obama ya bayyana Trump da 'sakarci'

Trump ya rasa goyon bayan manyan jam'iyyarsa

A farkon makon jiya ne shugaban ya soki Mika Brzezinski da kuma Joe Scarborough.

Kodayake, wasu daga cikin masu taimaka masa sun fara bayyana damuwarsu game da abubuwan da shugaban yake wallafawa a shafinsa na Twitter.

A ranar Asabar ne shugaban ya ce yana amfani da kafofi sada zumunta ne don ya isa kai-tsaye ga jama'a ba tare da mu'amala da kafafen yada labaran da aka saba da su ba, wadanda Mista Trump ya ke zargi da "yada labaran karya."

Hakazalika Trump ya soki kafar yada labarai ta CNN kamar yadda ya saba, bayan da ta janye wani labari da ta yi wanda yake cewa majalisar dokokin Amurka tana binciken wani mai taimakawa shugaban kasar.

Labarai masu alaka