Abin da ya faru a Afirka a makon jiya

Wasu kayatattun hotunan al'amuran da suka faru a Afirka a makon jiya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata 'yar wasan boksin din kasar Aljeriya yayin da take tsalle bayan ta doke takwararta Marline Niambongui 'yar Jamhuriyar Kongo a gasar Zakarun Damben Boksin na Afirka a birnin Brazzaville na Kongo a cikin makon jiya.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu magoya bayan jam'iyyar adawar kasar Kenya wato Nasa yayin wani taro a Nairobi a ranar Talata gabanin babban zaben kasar da za a yi a watan gobe...
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Nan wasu magoya bayan jam'iyya mai mulki ce a kasar Kenya wato Jubilee Party yayin wani gangami a birnin Nairobi ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wasu masu dafa burkutu a unguwar Koumassi a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadansu yara 'yan gudun hijira suna waka yayin wani babban taro kan 'yan gudun hijira a birnin Kampala na kasar Uganda.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mai tsaron gabar tekun Libya yana kallon wasu mutane 147 da aka ceto wadanda suke kokarin shiga nahiyar Turai ba bisa ka'ida ba ranar Talata.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wandansu mambobin kungiyar Black First Land First movement a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu yayin da suke wasa ranar Laraba.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadansu Musulmi suna sallar Idi a wani masallaci kusa garin Sale na kasar Morocco a ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadansu 'yan kasar Masar suna wasa bayan saukowa daga sallar Idi a wajen masallacin El-Seddik da ke birnin Alkhahira ranar Lahadi.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata Musulma yayin ana daf da yin sallar Idi a wani masallaci da ke yankin Ceuta na kasar Spain ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan uwa da abokan arziki suna alhinin wadanda harin wurin shakatawa na Campement Kangaba ya rutsa da su a kusa da birnin Bamako na kasar Mali.

Labaran BBC