India: Kun san matar da ta fuskanci harin acid sau biyar?

India
Image caption Ana yawan kai wa mata hari da acid a India

'Yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta India, sun ce wata an sake watsa wa mata sinadarin acid, wadda a baya ta taba fuskantar hare-haren acid din har sau hudu.

An kai wa matar hari na baya-bayan nan ne a wasu dakunan kwana na mata a babban birnin jihar Lucknow, duk da cewa, ya kamata 'yan sanda su rika ba ta kariya a ko wanne lokaci.

A 2008 ne aka fara kai wa matar wacce ba a bayyana sunanta ba hari, bayan an samu wata takaddama a kan mallakar wani gida.

Daga nan kuma, sai ta fuskanci wasu hare-haren, wadanda aka tsara su domin a matsa mata lamba ta janye karar da ta shigar kan cin zarafinta da aka yi na farko.

Daga baya kuma, aka bayar da belin wasu maza biyu da aka zarga da tilasta mata shan acid a cikin jirgin kasa.

Labarai masu alaka