An zargi Trump da tunzura cin zarafin 'yan jarida

Trump Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An hada bidiyon ne, daga wani bidiyon Mista Trump din, lokacin da yake kokuwa da wani mutun a gidan dambe

An zargi shugaban Amurka Donald Trump da na neman ingiza kai hari kan 'yan jarida, bayan ya yada wani bidiyon barkwanci, wanda ya nuna shi yana gabzan wani mutun da aka rufe kan shi da alamar tambarin kafar yada labarai ta CNN.

A cikin bidiyon, an nuna Mista Trump ya kayar da mutumin a kasa, sannan yake ta narkan shi.

Kafar watsa labaran ta CNN ta ce wannan rana ce ta bakin ciki, inda shugaban Amurka zai karfafa cin zarafin 'yan jarida ne.

Ta kuma ce halin yara da shugaban yake nuna wa, bai dace da girman ofis din shi ba.

Mista Trump dai ya sha sukar kafar ta CNN da wasu kafafen yada labarai, yana mai zarginsu da yada abin da ya kira labaran karya.

An hada bidiyon ne, daga wani bidiyon Mista Trump din, lokacin da yake kokuwa da wani mutun a gidan dambe wasu shekaru da suka wuce.