Ko taron ƙasashen G-5 na Sahel ya yi nasara?

taron kungiyar G-5 Sahel Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabanin kasashen kungiyar G-5 Sahel a taron Bamako na kasar Mali

Wasu masharhanta sun ce ƙasashe masu faɗa-a-ji kamar Faransa da sauran Tarayyar Turai suna da alhaki na tallafa wa rundunar ƙasashen yankin Sahel biyar don yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya da katse hanzarin 'yan Afirka da ke kwarara Turai a yankin.

Wani mai fashin baƙi kuma shugaban jami'ar Tawa a jamhuriyar Nijar, Farfesa Ado Mahamane na daga cikin masu irin wannan ra'ayi bayan wani taron ƙoli da ƙasashen suka gudanar ranar Lahadi a Mali.

Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Chadi da Burkina Faso da Mali da Muritaniya da Nijar da kuma shugaban Faransa, Emmanuel Macron.

Farfesa Ado ya ce daga cikin nasarorin da taron ya cim ma har da tabbacin da Faransa ta ba rundunar na taimaka mata wajen yaƙi da ta'addanci da kuma ci gaba da kasancewar sojojinta na Barkan.

Taron ya kuma ɗauki wani ƙuduri na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda ya karfafa aikin rundunar sojin ta yankin sahel, in ji Ado Mahamane.

A cewarsa abu ne mai wuya ƙasashen su yi aiki da dakarunsu kaɗai wajen gudanar da wannan gagarumin aiki.

"Babu ƙasar duniya wadda ita ɗaya za ta iya yakar wannan ta'addanci. Ta'addanci abu ne da ya maimaye duniya."

Ya kuma rikicin 'yan ta-da-ƙyar-baya da Mali ke fuskanta kamar wata wutar daji ce wadda matuƙar ba a kashe ta ba, tana iya kai wa har Faransa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Emmanuel Macron shugaban kasar Faransa

Farfesa Ado Mahamane ya ce akwai tabbacin cewa rundunar za ta samu kuɗin da take bukata da dakaru, don wanzar da zaman lafiya a yankin Sahel.

Ya ce ƙasashen Turai suna samun amfani a yankin sahel, ta hanyar haƙar ma'adanai kamar Uranium da zinare da ƙarafa don haka idan ba su sa hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sahel jarin da suka zuba ka iya salwanta.

Haka kuma, ya ce Nijar ƙasa ce da ke kewaye da ƙasashe masu fama da tashin hankali irinsu Nijeriya da Libya da kuma Mali.

Idan wannan shinge na tashin hankali da aka yi wa Nijar aka samu aka sare shi, ƙasar za ta samu ta walwala, kuma harkokinta za su ƙara ci gaba a samu bunkasa mai ɗorewa, in ji Farfesa Ado.

Labarai masu alaka