Muna nan muna ƙoƙarin kamo Shekau - Buratai

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya rundunar sojin Nijeriya ta sha cewa ta kashe Shekau amma daga bisani sai ya sake bayyana a faifai bidiyo

Dakarun sojin Nijeriya sun ce suna can suna ƙoƙari don su kama shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Babban hafsan sojan ƙasar, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce ko da yake, ba zai iya bayyana dabarun da suke ƙoƙarin yin amfani da su a nan gaba ba, amma za su ci gaba da kutsa kai duk inda 'yan Boko Haram suke.

A cewarsa, mutane na da hujjar su riƙa tunanin cewa rashin kamawa ko gamawa da Abubakar Shekau, tamkar an kashe maciji ne ba a sare kansa ba a yaƙin da Nijeriya ke yi da Boko Haram.

Buratai ya ce ba shakka hakan na buƙatar ƙarin haƙuri daga ɓangaren jama'a.

Ya kuma ce akwai buƙatar haɗin kai tsakanin sojoji da sauran jami'an tsaro don murƙushe 'yan ta-da-ƙayar-baya.

"Ba aikin soja kaɗai ba ne, dole akwai buƙatar sauran jami'an tsaro, mu ƙarfafa haɗin kai," in ji Janar Buratai.

Ya ce suna tattaunawa da 'yan sanda a baya-bayan nan, don ganin sun koma wasu garuruwan da suka fice a baya ta yadda sojoji za su ƙara dannawa dazuka.

Babban hafsan ya ce akwai buƙatar ƙarin dakarun soja da ke yankin arewa maso gabas, don kuwa waɗanda suke Borno da Yobe ba su kai dubu 50 ba.

Ya ce sojojinsa sun samu nasara don kuwa yaƙi a yanzu ba batu ne yawan dakaru ko yawan kayan yaƙi kawai ba.

"Sanin aikin ma shi ma yana cikin dabara(r yaƙi) da lura da haƙƙoƙin sojoji da samar da horo na musammam ga dakarun da za a tura fagen daga."

Labarai masu alaka