Aisha Buhari ta sake komawa London mijinta

Aisha Buhari Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari
Image caption Aisha Buhari ta shafe mako guda a London inda mijinta ke jinya

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta sake tafiya Birtaniya domin duba lafiyar mijinta Muhammadu Buhari wanda ya shafe makonni da dama yana jinya a can.

Wata sanarwa da mai magana da yawunta, Suleiman Haruna, ya fitar ta ce: "za ta isar wa shugaban sakonnin alheri da al'ummar kasar ke aika masa".

Ya kara da cewa a safiyar ranar Litinin ne Hajiya Aisha ta bar Najeriya amma sai Talata za ta isa London saboda za ta yada zango a kasar Habasha domin halartar taron matan shugabannin kasashen Afirka kan cutar kanjamau.

Kusan wata biyu kenan da Shugaba Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar zuwa Birtaniya - wadda ita ce tafiyarsa jinya karo na biyu a bana.

A watan da ya gabata ma ta ziyarci mijin nata inda bayan ta dawo ta shaida wa manema labarai cewa yana samun sauki sosai kuma ya kusa koma wa gida.

Tun bayan tafiyarsa, sau daya aka ji duriyarsa, lokacin da ya aike da sakon sallah ga al'ummar Musulmin kasar.

Rashin lafiyar shugaban tana ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus don fuskantar kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

Rashin lafiyar Buhari

Me kuka sani?

Yuni 2016

Ya tafi London don jinyar ciwon kunne inda ya shafe mako biyu.

Janairu 2017

Ya sake tafiya London inda ya shafe mako bakwai yana jinya.

 • Maris 2017 Ya koma Najeriya inda yace bai taba rashin lafiya kamar wannan ba.

 • Mayu 2017 Ya sake tafiya London kuma har yanzu yana can.

 • Yuni 2017 Matarsa Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai bayan da ta ziyarce shi.

Getty

Rashin lafiya ta mamaye rayuwar Buhari a 2017

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin lafiyar da yayi a farkon bana ta tsananta sosai
 • 19 ga watan Janairu ya tafi Birtania hutun jinya
 • 5 ga watan Fabreru ya nemi majilisa da ta tsawaita hutun nasa
 • 10 ga watan Maris ya dawo gida to sai dai bai koma aiki ba kai tsaya
 • 26 ga watan Afrilu ya kasa halartar taron majalasar zartarwa karo na biyu, inda ya rinka "aiki daga gida"
 • 28 ga watan Afurilu bai halarci Sallar Juma'a ba
 • 3 ga watan Mayu bai halarci taron majalisar zartarwa ba karo na uku jere
 • 5 ga watan Mayu ya halarci Sallar Juma'a a Abuja
 • 6 ga watan Mayu ya sake tafiya Birtaniya neman magani
 • 6 ga watan Yuni Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai

Labarai masu alaka