Ba ma goyon bayan Biafra – Shugabannin Igbo

Igbo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugabannin al'ummar Igbo a Najeriya sun yi watsi da fafutikar kafa kasar Biafra inda suka ce ba wannan ce matsalar da ke gabansu ba.

Sai dai shugabannin sun bukaci a sake fasalin kasar.

Sun bayyana hakan ne ranar Asabar yayin wani taro da Gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi ya kira karkarshin jagorancin kungiyar kare muradin kabilar Igbo wato Ohanaeze Ndigbo.

Taron ya samu halarcin duka gwamnonin yankin Kudu masu Gabashin kasar da shugaban kungiyar Ohanaze da kuma sauran masu fada a ji a yankin.

Igbo sun tsayar da al'amura kan Biafra

'Yan Biafra na zanga-zangar goyon bayan Trump

Me ya sa aka farfaɗo da son kafa kasar Biafra?

A wata takardar da aka fitar bayan taron, shugabanin sun bayyana cewa ba sa goyon bayan ikirarin ballewa daga Najeriya abin da aka fi sani da Biafra.

"Abin da muke nema bai wuce kasancewar Najeriya kasa daya, al'umma daya ba. Sai dai muna fatan ganin kasar da babu bambancin addini ko kabila ko kuma siyasa. San nan akwai daidaito a cikinta ta hanyar wanzar da adalci," in ji su.

Suka ci gaba da cewa: "Muna goyon bayan sakewa tsarin zamantakewar kasar fasali kuma muna kira ga gwamnati da ta gaggauta yiwuwar zartar da shawarwari da mahalarta taron kasa na shekarar 2014 suka bayar karkashin shugabancin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan."

Wasu na ganin watsi da fafutikar kafa kasar Biafra da al'ummar Igbon suka yi ba ya rasa nasaba da kire-kiren da jagoran da ke fafutikar kafa jamhuriyar Biafra Nnamdi Kanu ya yi cewe al'ummar yankin su kaurace wa zabe.

Al'marin da shugabanin ke wa kallon kokarin yi musu sakiyar da ba ruwa.

Har ila yau, akwai kuma masu kallon cewa wa'adin wata uku da gamayyar kungiyar arewacin kasar ta ba Igbo da su bar arewacin kasar shi ne ya jawo shugabannin kabilar suka dauki matakin nesanta kansu daga Biafra.

Labarai masu alaka