Dan Masanin Kano: Kun san tarihin Yusuf Maitama Sule?

Maitama Sule
Image caption Marigayi Maitama Sule ya rasu ne a kasar Masar bayan gajeruwar rashin lafiya

Kafin rasuwarsa a ranar Litinin, Dan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya taka rawa sosai a fannoni daban-daban a Najeriya, inda ya zamo daya daga cikin mutanen da suka fi fice da kuma kima a kasar.

An haifi marigayin ne a jihar Kano kimanin shekara 88 da suka wuce.

Marigayin shahararren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya taba rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya zama minista lokacin Firai Ministan Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.

Hakazalika, galibin mutane za su rika tuna wa da marigayin ta wajen yadda ya kware wajen iya magana.

A shekarar 1976 ne aka ba shi kwamishinan gwamnatin tarayya mai kula da korafe-korafen jama'a.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Marigayi Dan Masani Kano Maitama Sule akan batun juyin mulkin 1966

Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.

Har ila yau, gwamnatin Shagari ta nada shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.

A can ne ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.

Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zabe a shekarar 1983 ya sake nada shi Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shuagabn kasa kan yaki da cin hanci.

Image caption Maitama Sule ya zama minista lokacin Firai Ministan Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Balewa

An taba ruwaito shi yana cewa: "Kowane mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba 'yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi'u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa."

Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda 'yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.

A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.

Ya rasu ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu, mata shida.

Labarai masu alaka