Nigeria: Shugaban Majalisar Dokokin Kano ya yi murabus

Rurum Hakkin mallakar hoto Rurum Facebook
Image caption Ana zargin Alhassan Rurum da aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano a Najeriya Kabiru Alhassan Rurum ya yi murabus, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban ya yi murabus ne tare da mataimakin shugaban masu rinjaye Mai-fada Bello Kibiya.

Ana zargin Alhassan Rurum da aikata wasu laifuka da suka shafi cin hanci. Sai dai shugaban ya musanta aikata wani laifi.

Har ila yau, ya ce ya yi murabus ne saboda ya bayar da damar gudanar da bincike a kansa.

Daga nan ne sai 'yan majalisar suka zabi Abdullahi Yusuf Atta wanda yake wakiltar mazabar karamar hukumar Fage a matsayin sabon shugaba.

Labarai masu alaka