Amurka na takalar mummunan fada a iyakar ruwanmu — China

Wannan hoton jirgin yakin Amurka ne a lokacin da ya isa Shangai a 2015 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan hoton jirgin yakin Amurka ne a lokacin da ya isa Shangai a 2015

China ta zargi rundunar sojin ruwan Amurka da mummunan takalar faɗan siyasa da na soja a iyakar ruwanta.

China ta tura jiragen ruwa da na sama zuwa tsaunin da ake taƙaddama kansa don su gargaɗi jirgin ruwan yaƙin Amurka ya bar yankin.

Shugaba Trump ya zanta da takwaransa na China, Xi Jinping ta wayar tarho, kuma a bahasin da jami'ai suka bayar game da tattaunawar, babu shugaban da ya bijiro da tunzurin da shiga tekun ya haifar.

Sai dai mahukuntan Beijing sun ce Mista Xi ya sanar da Donald Trump cewa, akwai wasu "batutuwa marasa dadi" a dangantakar kasashensu kuma ya nuna kin amincewarsa ga manufar gwamnati a birnin Washington kan Taiwan.

Me ya faru a kusa da tsibirin Triton?

A wata sanarwa da aka fitar a ranar Lahadi da yamma, ma'aikatar harkokin wajen China ta tabbatar da rahotanni cewa jirgin ruwan yaki na Amurka ya shiga tekun da Chinar ke ikirarin cewa nata ne.

Kafar yada labarai ta Fox News ta ambato jami'an ma'aikatar tsaron Amurka na cewa, jirgin yakin ya yi tafiyar kilomita 12 daga gabar ruwan tsibirin Triton, a wani bangare na 'yancin da take da shi don yi wasu ayyuka a tekun.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da izinin cewa ko wacce kasa tana iya yin iko da ruwan har zuwa kilomita 12 daga gabar tekun ta bangarenta. Tafiyar da jirgin yakin Amurkan ya yi mai nisa na nuna cewa Amurkar ba ta amince da cewa wata kasa ta mallaki wani bangare na tekun ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
A 2015 ne BBC ta samu damar ganin hanyarsaukar jirgin China a yankin da ake takaddama kansa

Sai dai China ta ce za ta yi amfani da duk wata hanya da ta dace don kare tsaronta da martabarta.

Ta kuma zargi Amurka da cewa tana neman rigima a yankin, bayan kuwa tuni Chinar da makwabtanta suka yi kokarin kwantar da duk wani rikici da ke tasowa a yankin.

Haka kuma kasashen Vietnam da Taiwan suna ikirarin cewa tsibirin nasu ne. A shekarun baya-bayan nan China tana fuskantar takaddama tsakaninta da makwabtanta a kan mallakar wannan yanki na tekun.

Hakkin mallakar hoto China News Service

Takaddamar da aka sha fuskanta tsakanin mayan kasashen biyu masu kaerfin fada a ji

A watan Mayun 2017 jirgin yakin Amurka ya yi sintiri a kusa da yankin da ake takaddama a kansa a tsibiran da ke yankin

Mayun 2017 jiragen saman yakin China sun kama jirgin yakin Amurka a sararin samaniyar tekun gabashin China

Fabrairun 2017 Amurka ta fara sintiri a Kudancin Tekun China

Disambar 2016 China ta mayar wa Amurka jirgin yakinta maras matuki na karkashin ruwa

Mayun 2016 jiragen yakin saman China sun kama jirgin leken asiri na Amurka a sararin samaniyar Kudancin Tekun China

Fabrairun 2016 China na zargin Amurka da girke sojoji a Kudancin Tekun China

Labarai masu alaka

Karin bayani