Maitama Sule: A ina za a binne Dan Masanin Kano?

Dan masanin Kano

Za a yi jana'izar marigayi Dan Masanin Kano, Maitama Sule a ranar Talata a fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu a birnin Kano bayan an dawo da gawarsa daga kasar Masar.

Marigayin ya rasu ne bayan wata gajeriyar jinya da yayi dangane da ciwon zuciya, dalilin da yasa aka kai shi wani asibiti a kasar Masar domin kula da lafiyarsa.

Wakilin BBC Ibrahim Isa ya gana da Mukhtar Maitama Sule, daya daga cikin 'ya'yan marigayin. Ya fara da tambayar dan nasa lokacin da ya sami labarin rasuwar Dan Masanin.

"Da safe, kanina da yake tare da shi a Al-Kahira, shi ne ya bugo min waya ya sanar da ni."

BBC: Tun yaushe ne yake can Masar?

"Ranar Asabar da ta wuce a ka kai shi, kashegari, watau ranar Lahadi sai a ka kai shi dakin bai wa marasa lafiyar da ke cikin tsanani kulawa ta musamman wato 'Intensive Care', yau Litinin da safe kuma Allah Ya yi ikonsa."

BBC: Wane ciwo ne yayi masa sanadi?

Ciwon zuciya ne.

BBC: Kun sami ganawa da shi kafin tafiya da shi asibiti?

Ai ba wanda bai yi magana da shi ba, domin yana da natsuwa tare da shi. Yana magana, yana iya gane kowa.

BBC: Da wani abun da ya fada, da zaku iya tunawa, ko ya nuna wata ishara haka?

Duk wanda ya san shi, ya san a cikin addu'a yake kullum. Allah Yasa mu dace, Allah Ya yi muku albarka, wadannan sune kalamansa.

BBC: Wane irin gibi kake ganin marigayi ya bari?

Hakikanin gaskiya ba zai misaltu ba, saboda ni abokina ne shi. Abokantaka muke yi da shi. Babu irin maganar da bama yi da shi. Ya bani dama ta mu'amulla kwarai da gaske. Domin tun lokacin da ya sami larurar ido yace da ni, "ka dauke ni kamar abokinka, bani da mutum kamarka", ya kara da cewa "ina son ka kusa da ni a ko da yaushe".

BBC: Ta fuskar iyali, me ya bari a baya?

Ya bar matarsa, ya bar 'ya'ya goma, jikoki kuwa suna da dama.

BBC: Yana da shekara nawa ya bar duniya?

Shekararsa 88.

BBC: Yaushe za'a yi janaizarsa?

In Allah Ya yarda ranar Talata bayan an kawo gawarsa daga Masar, zuwa bayan sallar La'asar za a yi jana'izarsa.

Labarai masu alaka