Jihar Kano ta bayar da hutu don rasuwar Dan Masani

Danmasanin Kano Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alhaji Yusuf Maitama Sule ya yi gwagwarmaya a fannonin rayuwa da dama

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayar da hutun kwana daya na ranar Talata, don yin jana'izar marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule.

Kafin rasuwarsa a kasar Masar ranar Litinin, marigayin ya taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban a Najeriya, inda ya zamo daya daga cikin mutanen da suka fi fice da kuma kima a kasar.

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kano kan kafofin yada labarai Salihu Tanko Yakasai ya ce an ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutu saboda rasuwar tsohon fitaccen dan siyasar.

Hakazalika, a ranar Talatar ne za a yi jana'izar marigayin a mahaifarsa da ke jihar Kano bayan an dawo da gawarsa daga kasar Masar wurin da ya yi gajeruwar jinya.

Za a yi jana'izar ne da misalin karfe hudu na yamma a fadar Kano da ke Kofar Kudu a ranar Talatar.

Labarai masu alaka