Boko Haram sun sace mata da yara a Niger

Boko haram Hakkin mallakar hoto Getty Images

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar sun ce an kashe mutum tara da kuma sace wasu mata a kalla 40 a yankin kudancin kasar.

Al'amarin ya faru ne a daren ranar Lahadi a kauyen Ngalewa mai nisa kilomita 50 daga iyakar kasar da Najeriya wurin da rikicin Boko Haram ya fara.

"Mutum tara ne suka mutu kuma aka sace a kalla 30," in ji wani dan jarida Mamman Nour.

Har ila yau, magajin garin yankin Abba Gata Issa, ya tabbatar da cewa mutum tara ne suka mutu sandiyyar harin, yayin da kuma ya ce a kalla mata da yara 40 ne aka sace.

A makon jiya ne wani harin kunar bakin wake ya kashe mutum biyu da jikkata wasu 11 a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.

Kungiyar Boko Haram tana yawan kai hare-hare a garuruwan da ke kan iyakar Nijar da Najeriya.

Kimanin mutane dubu 20,000 suka rayukansu daga rikicin kungiyar Boko Haram shekara takwas da suka wuce.

Labarai masu alaka