Emmanuel Macron zai rage yawan 'yan majalisun Faransa

Zauren majalisa a Faransa
Image caption Akwai 'yan majalisar dokoki 385 da na wakilai 557 a kasar Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da yin garanbawul a cikin gwamnatin kasar, inda ya sanar da aniyar rage yawan 'yan majalisar dokokin kasar.

Da ya ke jawabi a urin tarihi na Palace of Versailles a kasar, ya ce ya na son rage kashi uku na 'yan majalisun.

Mista Mcron ya ce hakan zai sanya gwamnati ta rage yawan kudaden da ta ke kashewa, da samar damar yin ayyukan ci gaban al'uma.

Ya kara da cewa idan bai samu hadin kan 'yan majalisar ba daga nan zuwa shekara daya, to zai dauki matakin kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

A jawabin da ya dauke shi awa daya da rabi, matashin shugaban mai shekara 39 ya sha alwashin dawo da martabar kasar Faransar.

Aniyar ta mista Macron ta rage yawan 'yan majalisun, ya bayyana rage 'yan majalisar wakilai daga 577 zuwa 385, ya yin da zai rage 'yan majalisar dokoki daga 348 zuwa 232.

Labarai masu alaka