Senator Bukar Abba: Ba ruwan mutane da huldata da 'yan mata

Bukar Abba Hakkin mallakar hoto Sahara Reporters
Image caption Sanata Bukar Abba ya ce zai binciki yadda bidiyon ya yadu

Tsohon gwamnan jihar Yobe a arewacin Najeriya Bukar Abba Ibrahim ya ce neman bata masa suna ake yi shi ya sa aka fitar da bidiyon da yake tare da wasu 'yan mata tsirara a daki.

A hoton bidiyon da shafin Sahara Reporters ya wallafa, wanda ya rinka yawo a intanet, an nuna Bukar Abba wanda Sanata ne da ke wakiltar Yobe ta Gabas, yana sanya kayansa a gaban wasu 'yan mata, abin da ke nuna kamar ya yi lalata da su.

Amma a hirarsa da Premiuim Times, sanatan ya ce bai yi wani laifi ba a hukumance, kuma an fitar da bidiyon ne kawai a kokarin bata masa suna da son ganin bayansa.

A cewarsa "Wannan abu ne da ya shafi rayuwata, sirrina ne. Ina ruwan mutane da huldata da 'yan mata?

"Ka san mutane idan suna neman wani abu a wajenka ba su samu ba, to za su yi duk abin da za su yi don bata maka sun da yi maka bi-ta-da-kulli," in ji sanatan mai shekara 67.

Bidiyon mai tsawon minti biyu, wanda aka dauka a wani daki mai kama da otel, ya jawo ce-ce-ku-ce matuka a kasar, musamman a shafukan sada zumunta da muhawara.

Hakkin mallakar hoto Sahara
Image caption Kafar yada labarai ta Sahara ce ta fara wallafa bidiyon

An nuna wata mace daga cikin matan biyu tana rike da kamara tana daukar abin da ke faruwa, yayin da dayar kuma take zazzagawa cikin dakin. Sai dai dukkansu da tufafi a jikinsu ba kamar Sanata Bukar ba.

Amma Sanata Abba ya ce ba zai iya tuna lokaci da kuma wajen da ya yi wata huldar banza da wasu 'yan mata ba, duk da cewa bai musanta cewa shi ne a bidiyon ba.

Ya kara da cewa, babu wanda yake bin sa bashin rantsuwa balle ya tsaya yin jawabi don bai aikata wani mugun laifi ba.

"Idan da cewa suka yi na yi wa wata fyade, to da sai ya zama wani batu daban. Ko kuwa dai kasancewa ta wani babban jami'in gwamnati sai ya hanani jin dadin rayuwata?"

Sanata Abba ya ce ya san lokacin da daya daga cikin 'yan matan ke daukar bidiyon, amma sai ta ce masa kawai wasa take yi tana haska dakin ne da kamara.

"Kawai ce min suka yi wasa ne ni kuma sai ban dauki al'amarin da wani muhimmanci ba. Wannan wani abu ne da ya faru tsakanin mutane biyu da suka mallaki hankalin kansu."

Hakkin mallakar hoto Sahara Reporters
Image caption A bidiyon an nuna hoton daya daga cikin 'yan matan

Sai dai Sanata Bukar ya ce ba zai bar maganar ta mutu a haka ba, dole zai yi bincike kan yadda aka yi bidiyon ya bayyana.

A watan Yunin shekarar 2016 ma gwamnatin Amurka ta zargi wasu 'yan majalisar wakilan Najeriya da neman karuwai a lokacin da suka kai wata ziyarar aiki kasar.

Wata wasika da jakadan Amurka a Najeriya, Mr. James Entwistle, ya aikewa shugaban majaliasar wakilan, Yakubu Dogara, ya zargi 'yan majalisa uku daga cikin goma da suka kai ziyara kasar da nuna rashin kamala da yunkurin yin fyade da neman karuwai.

Sai dai 'yan majalisar wakilan sun musanta zargin suka kuma bukaci Amurka ta kawo hujja.

Sanata Bukar Abba Ibrahim ya yi gwamnan jihar Yobe a karo biyu, daga shekarar 1999-2007. Matarsa Khadija Bukar Abba ita ce karamar ministar harkokin wajen Najeriya a yanzu.

Labarai masu alaka