Tsuntsaye sun tilasta wa jirgin sama saukar gaggawa

The AirAsia X plane on the tarmac at Brisbane Airport Hakkin mallakar hoto ABC
Image caption Fasinjoji sun ce sun ga wuta tana fita daga injin jirgin

Wasu tsuntsaye sun tilasta wa jirgin saman AirAsia X sauya akalarsa, inda ya yi saukar gaggawa a kasar Australia maimakon sauka a birnin Kuala Lumpur na Malaysia.

Fasinjoji 359 da jirgin yake dauke da su sun shiga rudani bayan jirgin ya tashi daga birnin Gold Coast na Australia ranar Litinin.

An ruwaito cewa an rika jin kara da tartsatsin wuta daga injin jirgin gabanin ya yi saukar gaggawa a birnin Brisbane sa'a guda bayan tashinsa.

"An samu wasu tsuntsaye biyu a kan titin jirgin," in ji kamfanin jirgin.

Wani fasinja da ke cikin jirgin ya ce, "na ji kara sau hudu zuwa biyar gabanin na ga wuta daga waje."

Ya ci gaba da cewa: "Daga nan ne sai jirgin ya fara jijjiga, sai kuma mu ji wata kara mai karfi," kamar yadda ya bayyana wa kafar yada labaran Sydney Morning Herald.

Har ila yau, wani fasinja mai suna Eric Lim ya ce al'amarin ya faru ne jim kadan bayan tashin jirgin.

"Kara muka rika ji daban-daban yayin da mutanen da ke cikin jirgin suka rika fasa kururuwa," kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook.

Shugaban Kamfanin Jirgin Benyamin Ismail, ya ce an tanadi wani jirgin wanda zai kwashe fasinjojin jirgin zuwa birnin Kuala Lumpur.

Ko a makon jiya ma, sai da aka sauya akalar wani jirgi na kamfanin bayan ya fuskaci matsalar inji, inda ya rika jijjiga yayin da yake sama.

Labarai masu alaka

Karin bayani