Uganda: An hana mata bayyana tsiraici da karin gashi a ofisoshi

Haka kuma na hana sanya tufafi mai kalar da ke da jan hankali zuwa ofis Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Haka kuma na hana sanya tufafi mai kalar da ke da jan hankali zuwa ofis

Gwamnatin Uganda ta fadawa ma'aikatan gwamnati cewa sun riga shiga ta mutunci kuma ta gargadi mata a kan kada su rika shigar da za ta nuna kirjinsu.

Ana dai ganin sabbin ka'idojin sun fi mayar da hankali ne kan mata ma'aikatan gwamnati.

Sanarwar ta fito karara wajan hana mata saka takalma marasa tsini, idan ba likita ne ya bukaci su yi hakan ba saboda lafiyarsu.

An kuma hana matan yin shigar da za ta nuna cibiyarsu da kuma rina gashinsu da kala mai haske ko kuma su saka karamin siket ko riga guntuwa.

A dayan bangaren kuma an bukaci maza su rika saka kwat da nek taya tare da yin aski, kuma an hanasu su saka riguna ko shet masu kala mai haske.

Kawo yanzu dai babu cikakaken bayani kan dalilin da yasa aka bada wannan umurnin yanzu ba.

Karin bayani kan matakin

Sanarwar dai ta kasance karara. Kar mata su sa takalma masu kananan diddige,sai dai in hakan na da nasaba da rashin lafiya, kar kuma su nuna kirjinsu ko kuma cibiya, kada kuma su rina gashinsu da wata kala mai haske; kar kuma su sa dangalallen siket ko guntayen riguna.

An sheda wa maza su rinka shiga ta bakaken tufafi, kar kuma su je aiki da takalma kafa - bude.

Sanarwar wani kokari ne na aiwatar da wasu dokokin da ake da su, to amma galibi ake watsi da su.

Sanarwar ta ce ma'aikatan gwamnati na saka kaya bisa tafarkin da ke bata sunan aikinsu.

Jami'ai dai na kallon Uganda a matsayin wata kasa dake bin tafarkin 'yan mazan jiya.To amma ba a san dalilin da ya sa aka bayar da umurnin a halin yanzu ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC