Na bar wadanda suka yi min sharri da Allah – Bukar

Bidiyon ya nuna Sanata Bukar tsirara Hakkin mallakar hoto Sahara
Image caption Bidiyon ya nuna Sanata Bukar tsirara

Sanata Bukar Abba Ibrahim ya shaida wa BBC cewa sharrin siyasa ne ya sa aka bayyanar da wani bidiyo da ke nuna shi tsirara, tare da wasu 'yan mata biyu.

Tsohon gwamnan Yoben ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da sashen Hausa na BBC ranar Talata, bayan da kafar yada labarai ta Sahara Reporters ta fara wallafa bidiyon a intanet har ya bazu tamkar wutar daji, ya kuma jawo ce-ce-ku-ce a kasar.

A ranar Litinin din ne kuma kafar yada labaran Premium Times ta wallafa wata hira da ta ce ta yi da sanatan, inda ya amsa cewa lallai ya san da batun bidiyon amma a tsammaninsa 'yan matan da yake tare da su a lokacin wasa suke yi.

A hirar tasa da BBC, Sanata Abba ya ce, "Ni dai ban ga bidiyon ba amma yadda nake jin bayani shiri ne na 'yan adawar siyasa, kuma a siyasa wannan ba sabon abu ne ba ne, komai suke yadawa ni bai dame ni ba."

Da ka tambaye shi ko wadanne 'yan siyasar yake zargi tsakain na jiharsa da na tarayya? Sai ya ce, "Yanzu ban tabbatar ba tukunna, amma muna bincike mu tabbatar daga inda abin ya taso da kuma wadanda suka shirya shi.

"Karamar yarinyar da ake kama sunanta na tabbata ba ita ta shirya wannan abun ba. Saboda haka za mu samu daidai wadanda suke bayan wannan abu. Kuma idan lokaci ya yi za mu bayyana mutane su ji.

"Amma mutane su yi hakuri gaskiya za ta fito insha Allahu."

Sai dai duk da haka, Sanata Bukar ya ce shi ba shi da niyyar daukar wani mataki na shari'a kan wadanda suka yi wannan abu, ya bar su da Allah kawai.

Hakkin mallakar hoto Sahara

"Ba ni da wani matakin komai, wannan abu kamar yadda na fada maka shiri ne na 'yan siyasa, shiri na 'yan adawa ne kuma zan barsu da Allah. Dole idan mutum ya dogara da Allah to gaskiyarsa za ta fito.

"Mun sha ganin irin wadannan abubuwa, kuma yau gashi Allah ya kawo gare mu," in ji Sanatan.

Ya ci gaba da cewa, "Ni ban san wadannan matan da suke magana akai ba, ban sansu ba, ban taba ganinsu ba, kuma hoton ma da suke yadawa ni ban ganshi ba ma har yanzu. Ko wa yai min magana sai ya ce ba shi da shi.

"Har yanzu babu wanda ya zo ya nuna min. Ni kuma dama ba na wani WhatsApp ko harkar intarnet. Waya kawai nake yi, idan an buga min na dauka, idan an yi min tes na bada amsa. Ban da wannan ba abin da neke yi da waya."

Ga dai sauran bayanin da ya yi wa BBC a hirar da ya yi da abokin aikinmu Naziru Mika'ilu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hira da Sanata Bukar Abba Ibrahim domin bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.