Ni ban bai wa 'yan majalisar Kano cin hanci ba – Dangote

Dangote Hakkin mallakar hoto Getty Images

Attajirin dan kasuwar da ya fi kowa arziki a Afirka, Aliko Dangote, ya ce zargin bayar da cin hancin da ake masa "ba gaskiya ba ne."

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin jihar Kano ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki zargin da ake wa attajirin kan bai wa majalisar kudi don su dakatar da binciken da suka fara a kan masarautar Kano.

"Kada kwamitin ya bata lokaci wajen bincike Dangote don zargin da ake masa duka ba gaskiya ba ne," in ji mai magana da yawunsa Tony Chiejina.

Ya ci gaba da cewa, "zarge-zargen duka ba su da tushe balle makama. Karya ce tsagwaronta. Zargin abin kunya ne ga Dangote," kamar yadda ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ranar Litinin.

A ranar Litinin ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Kabiru Alhassan Rurum ya yi murabus don bayar da damar gudanar da bincike game da zargin karbar cin hanci daga hannun Dangote.

Sai dai tsohon shugaban majalisar dokokin ya musanta karbar cin hancin. Kuma ya ce wasu ne suke kokarin bata masa sunana.

A watan jiya ne majalisar dokokin jihar ta dakatar da bincike a kan masautar Kanon.

Rahotanni sun ce tsohon shugaban majalisar ya ce shiga tsakanin da Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi da wasu manyan mutane a Najeriya na bukatar a dakatar da binciken an yi sa ne ta hannun gwamnatin jihar Kano, amma ba majalisa ba.

"Gwamna ne ya bukaci mu dakatar da binciken a madadin al'ummar jihar Kano."

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa wani kwamitin mutum biyar wanda zai binciki tsohon shugaban majalisar.

Alhaji Rurum ya ce ya yi murabus din ne don kare kimarsa da ta jama'ar da yake wakilta, kamar yadda ya bayyana wa NAN.

Labarai masu alaka