Yaushe Ali Nuhu zai daina rawa da waka fim?
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yaushe Ali Nuhu zai daina rawa da waka a fim?

Fitaccen mai shirya fina-finan Hausa Ali Nuhu Mohammed yace zai daina rawa da waka a fina-finan Hausa idan lokaci ya yi.

Jarumin mai kuma shirya fina-finan na Hausa ya ce yana yin rawar da waka ne kawai idan akwai bukatar haka a cikin fim.

Ya ce a yanzu ya rage yawan rawa da yake yi a fina-finan idan aka kwatanta da baya.

Ali Nuhu ya ce a matsayinsa na jarumi, yanayi ne ya ke sa shi yin rawa a cikin fim din Hausa.

Ya kara da cewa zai daina rawa da waka idan lokacin da ya kamata ya daina ya yi, to sai dai bai bayyana ko wane lokaci ne zai daina rawar ba.

A kwanan nan ne dai Ali Nuhu ya fara nuna wani fim mai suna Mansoor a gidajen Kallo, fim din da ake ga ya kawo sauyi a harkar fina-finan Hausa.

Labarai masu alaka