An yi jana'izar Dan Masanin Kano

Dan masani

Asalin hoton, Kano State Government

An yi jana'izar marigayi Alhaji Yusuf Maitama Sule bayan an yi masa sallah.

Farfesa Sani Zaharadeen ne ya jagoranci sallar a fadar Sarkin Kano, kuma dubban mutane ne suka halarci sallar jana'izar.

Cikin manyan mutanen da suka halarci jana'izarsa har da Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da gwamnonin Jihonin Kano da Bauchi da kuma attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote.

Marigayi Yusuf Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya rasu ne a ranar Litinin a wani asibiti da ke kasar Masar.

Kafin rasuwarsa a ranar Litinin, Dan masanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya taka rawa sosai a fannoni daban-daban a Najeriya, inda ya zamo daya daga cikin mutanen da suka fi fice da kuma kima a kasar.

Marigayin shahararren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya taba rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya.

Ya zama minista lokacin Firai Ministan Najeriya na farko Alhaji Abubakar Tafawa Balewa.

Hakazalika, galibin mutane za su rika tuna wa da marigayin ta wajen yadda ya kware wajen iya magana.

An taba ruwaito shi yana cewa: "Kowane mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba 'yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi'u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa."

A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.

Ya rasu ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu, mata shida.