Muna bukatar Fashola ya bayyana gaban majalisa

Fashola na daga cikin gwamnonin da suka yi wa shugaba Buhari mubaya'a
Image caption Fashola shi ke rike da manyan ma'aikatu a Najeriya

Majalisar wakilan Najeriya ta gayyaci ministan Makamashi da ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola domin ya yi mata karin haske kan maganganun da ta ce yana yi game da sauye-sauyen da aka gabatar a kasafin kudin kasar na bana.

A baya-bayan nan dai an ta yin musayar kalamai tsakanin majalisar da tsohon gwamnan na Legas, inda ya zarge su da sauya wasu manyan ayyukan da ma'aikatarsa ta shirya gudanarwa.

Sai dai 'yan majalisar sun nace cewa dokar kasa ce ta basu damar yin hakan.

Hon Adam Jegaba daga jihar Kaduna,ya shaidawa BBC cewa kundin tsarin mulki ya ba su damar yi wa ministan kiranye.

Ya kara da cewa duk kurarin da ake yi, kan irin ayyukan da aka ce Fashola ya yi a jihar Lagos a lokacin da ya ke gwamna, amma anan ya kasa yin wani abun a zo a gani.

Jagaba ya ce gwamnati ta dauki manyan ma'aikatun da ake bukatar yin gagarumin aiki amma hakan ba ta sa mu ba.

Ya ce a baya kallon kitse ake wa rogo, shi ya sa aka ba shi wadannan ma'aikatun.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin bangaren minista Babatunde Fashola dan jin martanin da za su maida, amma hakan ba ta samu ba.

Amma za mu kawo martaninsa a shirye-shiryenmu na gaba.

Labarai masu alaka