Ana 'wulakanta marayu da wawure tallafinsu a Zamfara'

Gwamna Abdul'aziz Yari
Image caption Ana zargin kwamishinar matan da laifin korar wasu daga cikin yaran da ke gidan marayun

Masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara a jihar Zamfara ta Najeriya, na ci gaba da kira ga mahukuntan jihar da su binciki zarge- zargen gallazawa marayu a gidan Marayu na jihar.

Akwai dai zarge-zargen cewa jami'ai na karkata akalar kayan abincinsu tare da barinsu da yunwa da ma batar da wasu yaran.

Wani mutum da ke makwabtaka da gidan marayun, shi ne ya wallafa wani sakon murya a shafin sada zumunta, shi ya janyo zazzafar muhawara kan halin da yara ke cikin a gidan marayu.

Wakilin mu Haruna Shehu Tangaza da ya zanta da mutum, inda ya kara jaddada abun da ya faru kan idon sa suka faru.

Mutumin ya yi zargin kwamishinar mata da walwalar jama'a ta jihar ita ke karkatar da akalar kayan da aka kai wa marayun, ciki har da kayan da jama'a ke kawo musu tallafi, da kayan abincin da gwamnati ke kawo wa.

Ya kuma yi ikirarin yara kanana na cikin mawuyacin hali na rashin tsafta da kulawa, yaran na gararanba a cikin gari.

Wasu kuma ana zargin su na yin aikatau a gidajen masu kudi, wasu na cewa ma an kori wasu daga cikin 'yan matan da ke gidan.

To sai dai kuma a martanin da ta mayarwa manema labarai Hajiya Balkisu Ibrahim, ta musanta zarge-zargen.

Ta kara da zayyana irin kayan abincin da ake dafawa marayun a kowanne wata da suka kama da shinkafa, da masara da taliya da sauransu.

Labarai masu alaka