'Yan majalisa sun dakatar da nadin mukaman da Osinbajo ya aika

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osibanjo
Image caption Kalaman mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo bai yi wa wasu 'yan majalisar dadi ba

Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da sauraron duk wani nadin mukami da bangaren zartarwa ya mika mata, har sai mukaddashin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya janye kalamansa na cewa majalisar na da takaitaccen iko wajen nadin mukamai a kasar.

Hakan ya faru ne a zaman da majalisar ta yi a ranar Talata bayan kammala hutun sallah karama, inda ta bukaci sai an bi ka'idodin da kundin tsarin mulki ya shimfida a kan nadin mukamai sau da kafa.

A watan Afrilun da ya gabata ne dai, mukaddashin shugaban kasar ya ce, bai kamata a mika sunan Ibrahim Magu ga majalisar domin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ba, saboda majalisar na da takaitaccen iko, kalaman da ba su yi wa 'yan majalisar da dama dadi ba.

Daya daga cikin 'yan majalisar ya bayyana cewa idan har mukaddashin shugaban kasa ya ce ba su da ikon tabbatar da mukamin wani, sai kuma daga baya ya turo mana takardar bukatarsu su tabbatar da wani mukamin, shin wanne ne za su bi?

Ya kara da cewa kamata ya yi majalisar dokoki ta dauki matakin dakatar da batun nade-nade mukamai, har sai an warware wannan takaddama.

'Yan majalisa sun mayar da martani ne bayan mukaddashin shugaban kasar ya nemi su amince da sunan mista Lanre Gbajabiamila a matsayin shugaban wata hukuma.

A lokacin rubuta wannan rahoto dai, ofishin mukaddashin shugaban kasar bai mayar da martani game da matsayin na majalisar dattawan Najeriya suka dauka ba.

Labarai masu alaka