Saudi Arabia da kawayenta za su gana a kan Qatar

Saudiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saudiyya da kawayenta na barazanar sanya wa Qatar karin takunkumi

Ministan harkokin wajen Saudi Arabia zai isa birnin Alkhahira inda zai tarar da takwarorinsa na Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain domin tattauna batun Qatar.

Taron na ranar Laraba na zuwa ne makonni hudu bayan kasashen sun yanke hulda da ita bisa zarginta da taimaka wa 'yan ta'adda.

Zargin da Qatar din ta musanta tare da yin watsi da sharuddan da suka gindaya mata.

A ranar Talata ne kwararru kan samar da bayanan sirri na kasashe hudun suka yi wata ganawa duk dai a kan Qatar.

Cikin sharuddan da kasashen suka gindaya wa Qatar har da dakatar da dangantaka tsakaninta da Iran, sannan ta rufe sansanin sojin Turkiyya.

Haka kuma sun bukaci Qatar ta rufe gidan talbijin dinta na Al Jazeera.

Kasashen sun ce tun da Qatar ta ki yin hakan to ta saurari martanin da zai biyo baya.

Labarai masu alaka