An zargi Saudiyya da 'yada ta'addanci' a Birtaniya

Man holding Islamic State flag Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ofishin jakadancin Saudiyya a Birtaniya ya ce kasar kanta na fama da hare-haren ta'adanci daga kungiyoyin al-Qaeda da IS

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa Saudiyya ce ke rura wutar yaduwar tsattsauran ra'ayin addini a Birtaniya.

Kungiyar kwararru ta Henry Jackson Society ta ce, "Akwai alaka mai karfi" tsakanin kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addini ta yadda suke samun kudi, da masu da'awa mai tsauri da kuma kungiyoyin jihadi da ke yada ta'addanci.

Kungiyar ta kasar waje ta yi kira da a yi bincike game da rawar da Saudiyya da sauran kasashen yankin Gulf ke takawa.

Sai dai ofishin jakadancin Saudiyya a Birtaniya ya ce zargin "karya ce karara".

A halin yanzu, ana ta matsa wa ministoci lamba da su wallafa nasu rahoton game da kungiyoyin ta'addancin da ke Burtaniya.

An dai bayyana cewa har yanzu ba a kammala rahoton da tsohon Firai minista David Cameron ya sa aka yi game da samuwa da kuma tasirin kungiyoyin jihadi a kasar ba.

Masu suka na ganin cewa hakan zai kawo rashin jituwa ga gwamnatin, wacce ke da kyakkyawar alaka da kuma karfin diplomasiyya, da tsaro, da kuma cinikayya da kasashen yankin Gulf, musamman Saudiyya.

'Tsaurin ra'ayi''

Kungiyar Henry Jackson Society, kungiya ce da ke tallata manufofin kasashen waje ta hanyar yada dimokradiyya, da bin doka da kuma tattalin arziki.

Rahoton nasu ya ce kasahen yankin Gulf, tare da Iran, na samar da kudi ga masallatai da cibiyoyin ilimin addaini wadanda ke taka rawa wajen samar da masu yada da'awar ta'adanci kuma ana alakanta su da samar da kayayyakin ayyukan da'adancin.

Rahoton ya zargi Saudiyya wacce take babbar kawar Birtaniya a yankin Gabas Ta Tsakiya, kuma babbar abokiyar huldar kasuwacinta.

Rahoton ya zargi daidaiku da kuma kungiyoyi da cewa suna taimakawa wajen yada abin da ta kira "tsattsauran ra'ayin Wahabiyanci", inda ya kawo misalai masu dumbin yawa.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Saudiyya a Birtaniya ya fitar, ya ce duk wani zargi da ke nuna cewa masarautar na marawa ta'addanci baya ba shi da tushe, kuma babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna haka."

Ta kuma nuna cewa kasar kanta na fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyoyin al-Qaeda da IS.

Ta kara da cewa: "Ba ma yi kuma ba za mu yarda da ayyuka ko ra'ayoyin ta'addanci ba, kuma ba za mu kwanta ba har sai mun ga bayan wadannan 'yan ta'adda da kungiyoyinsu".

Ma'akatar cikin gida ta Birtaniya ta ce zai iya yanke daukar nauyin ta'addanci, amma ya ki cewa komai game da rahoton.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Theresa May ta ce ta ce dangantaka tsakanin kasahen biyu na da matukar muhimmanci ga tsaro, da harkokin kasuwancin Burtaniya

A ranar Laraba ne dai ministocin kasashen wajen Larabawa ke ganawa a birnin Alkahira domin tattauna yiwuwar kara kakaba wa kasar Qatar karin takunkumi, yayin da ministan wajen Qatar din ke nasa taron manema labarai a birnin London.

Firai ministar Burtaniya Theresa May, wacce ta ziyarci Saudiyya a watan Afrilu ta ce dangantaka tsakanin kasahen biyu na da matukar muhimmanci ga tsaro, da harkokin kasuwancin Birtaniya.

Shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn ya yi kira ga Birtaniya da ta gaggauta tsayar da sayar wa Saudiyya makamai saboda tarihin kasar na keta hakkin bil-adama da kuma yadda sojojinta ke yaki a kasar Yeman.

Labarai masu alaka

Karin bayani