Abaya: Wasu matan Saudiyya sun kalubalanci malami

Mata sanye da rigunan abaya Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Mata sanye da rigunan abaya

Wani shahararren malamin addinin Musulinci a kasar Saudiyya Mohammed Alarafe ne, ya kawo shawara a kan batun da ya shafi abaya, tufafin da ya fi dacewa wanda yake rufe dukkanin jiki in ban da fuska da kafa da kuma tafin hannu.

An fi saka irin wannan riga a kasashen da suke da Musulmai da yawa, kuma dogayen rigunan na da tsari daban-daban da kuma kaloli.

A ranar Lahadi ne Mista Alarafe ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, "Ku mata; kada ku sayi duk wata abayar da take da ado a jikinta. Ko wacce aka kayatata, ko mai tsaga, kuma kada ku bayyana jikinku. Don Allah mata kada ku bayyana ko wacce kwalliya, kuma ka da ku yi kwalliya irin ta zamanin Jahiliyya."

Mata da yawa na yi wa malamin gatse ta hanyar tura hotunan abayoyinsu suna tambayar Dakta Arifi a kan amincewarsa wajen amfani da su.

Duk da haka, ya sha bayar da shawarar tasa a shafin Arab Twitter sama da sau 31,000, yawancinsu suna zaune a kasashen Gulf.

Hakkin mallakar hoto Empics
Image caption Wata mai amfani shafin twitter na neman shawarar malamai a kan abayarta

Wata mace ta turo hoton rigarta tana tambaya: "Malam ya ka ke ganin rigata? Nan gaba, zan sayi mai kwalliya da take da tsaga a jikinta. Zan yi kokari na sayi abayar da mutanen zamanin Jahiliyya ba su saka irinta ba."

Yayin da ita ma wata mai amfani da shafin Twitter ta yi tambayar cewa ko ba za ta iya amfani da abayarta ita ba, duk da cewa ba a Saudiyya take da zama ba."

Image caption Kayan ado na kayatarwa da ake amfani da su wajen dinka abaya

Sai dai a wurin wasu mazauna kasar suna daukar abaya a matsayin wani abu na Musulunci ba wai abin gayu ba.

Shawarar za ta kawo ce-ce- kuce ne kawai a kasashen da suke da tsattsauran ra'ayi, amma a ka'ida matan da suke Saudiyya ana sa ran za su rufe adonsu daga idon maza.

A watan Disambar shekarar 2016 ne aka nuna hoton wata 'yar Saudiyya da take tsaye a kan titin Riyadh ba tare da ta saka abaya ba, inda hakan ya haddasa ce-ce-kuce a shafukan sa da zumunta.

Hoton da aka tabbatar da cewa na wata mata ne da ake kira da Malak, ko Angel Al Shehri, wanda ya jawo samun sakonni sama da 9,000 a shafin Twitter inda mutane ke kira da a kamata.

Labarai masu alaka