Dole Buhari da Osinbajo su bayyana sunayen 'barayi'

Osinbajo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mukaddashin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya fara jan ragamar kasar ne bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi hutun jinya Birtaniya

Wata babbar kotu ya tarayya da ke a Legas ta umarci shugaban Naijeriya Muhammadu Buhari da mataimakinsa professor Yemi Osinbajo da su bayyana sunayen mutanen da aka kwato kudaden gwamnati a hannunsu.

Mai shari'a Hadiza Rabiu Shagari ta kuma nemi gwamnatin kasar ta bayyanawa 'yan Naijeriya adadin yawan kudin da aka kwato daga hannun barayin gwamnatin.

Kungiyar nan mai neman kawo daidaito da kare hakkin bil'adama ta SERAP ce ta shigar da kara a gaban babbar kotun inda ta nemi ta umarci gwamnatin tarayya ta bayyana manyan ma'aikatan gwamnati da ake zargi da yin babakere da baitulmalin Najeriya a yayin da suke a kan mulki.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari dai ta ce ta kwato biliyoyin nairori- to amma ba a bayyana ko daga hannun mutanen da aka kwato su ba.

A baya bayan nan dai wasu manyan kotu na a kasar sun mallakarwa gwamnatin tarayya kudade har naira biliyan 15 da aka gano a wani katafaren gidan alfarma a Ikoyi da kuma kudade sama da dala miliyan tara da aka gano a inda tsohon manajan daraktan kamfanin NNPC, Andrew Yakubu ya boye su.

Labarai masu alaka