Lionel Messi ya amince ya tsawaita kwantaraginsa a Barcelona

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto EPA/Reuters
Image caption Lionel Messi ya ci kwallo 507 a wasan da ya buga wa Barcelona

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi ya amince ya tsawaita zamansa a kulob din har zuwa shekarar 2021.

Dan wasan mai shekara 30, wanda ya koma Barca lokacin yana da shekara 13, zai sanya hannu a sabon kwantaragi idan ya koma atisaye daga hutun da yake yi.

Kulob din da ke buga wasan La Liga ya ce, "Kulob din nan na matukar farin ciki da sabunta kwantaragi da Messi zai yi, kasancewarsa gwanin dan wasa na tarihi."

Dan wasan dan kasar Argentina ya ci wa kulob din kwallo 507 a wasa 583 da ya buga unda ya soma kwallo a kulob din a 2004, abin da ba a taba yi ba.

Messi, wanda yanzu haka yake hutun angwanci bayan auren da ya yi wa budurwarsa tun suna kanana Antonela Roccuzzo,shi ne wanda ya fi zura kwallo a gasar La Liga inda ya ci kwallo 349.

'Mahadi mai dogon zamani'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan shi ne karo na takwas da Messi zai sanya hannu a kwantaragi da Barca tunda ya koma kulob din yana dan shekara 13

Kafofin watsa labaran Spain sun ce za a bai wa dan wasan yuro 300m a sabon kwantaragin nasa bayan da a watan Mayu Messi ya ki amincewa da kudin da aka yi tayin ba shi.

A watan sanarwa, Barca ya ce Messi ya "jagoranci kulob din ya samu nasarar da bai taba samu ba a tarihin kwallon kafar duniya".

"Leo Messi baitsaya a nan ba - dan kasar ta Argentina yana kan ganiyarsa don haka yana da muhimmiyar rawa da zai ci gaba da takawa, abin da dukkan magoya bayan Barca ke son ji, wato ya kara akalla shekara hudu yana cin karensa babu babbaka," in ji sanarwar.

A baya dai kwantaragin Messi za ta kare ne a 2018.

An yi ta hasashen cewa dan wasan zai koma Manchester City amma sabon kwataragin nasa zai sa ya ci gaba da zama a kulob din har lokacin da ya kai shekara 34.

Labarai masu alaka