Ko bikin Manchester zai iya sa mata su mallaki duniya?

Protesters dressed like the G20 leaders return backstage from their appearance during a demonstration against the upcoming G20 economic summit during a protest march on July 2, 2017 in Hamburg, Germany Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu zanga-zanga suna amfani da fuskokin shugabannin kasashen kungiyar kasashe masu arzikin masana'antu G20.

Me zai faru idan mata suka samu madafun iko a duniya: Wannan shi ne taken taron bikin baje kolin fina-finai a birnin Manchester na kasar Birtaniya.

Taron wanda taurarin fina-finai suka halarta an shirya shi ne domin yin nazari kan ko mata za su yi abin da maza suka kasa yi, na game da warware matsalolin duniya.

"Na yi imani cewa duniya za ta fi samun ci gaba idan da a ce mata ne suke mulkinta"

Wannan shi ne matsayin Vicky Featherstone, wacce darakta ce a gidan wasa na Royal Court, gidan wasa mafi girma a birnin Landan.

Ita ce mai ba da umarni a shirin me zai faru idan da mata zalla ne suke mulkin duniya?, wani shiri da za a nuna kai-tseye a bikin baje kolin kasa-da-kasa na Manchester.

Ta ce: "Ina ganin da al'amura za su sauya. Shakka babu."

Hakkin mallakar hoto Moviestore/REX/Shutterstock
Image caption 'Ina tunanin akwai bukatar daidaito tsakanin maza da mata'

Muna magana ne lokacin wani dan hutu, na kuma tambayi Featherstone matsayinta game da taken wasan, ko tana ganin duniyar za ta zauna lafiya. Sai ta amsa tambayar da tambaya.

"Za ka yi?"

Mece ce amsar? Shin zan kaskantar da jinsina in ce na yarda?

Ko idan na ki amincewa, zan karyata dubban shekarun danniya, da kuma nuna cewa ban yadda da abin da ake ciki ba a duniya da maza suke jagoranta.

Ina tunanin muna bukatar daidaito ne, na sha cewa mu ba ma son a rika nuna bambanci.

"Na yarda. Ni a ganina taken bai yi ba. Muna bukatar daidaito ne. A ganina haka batun yake.

Hakkin mallakar hoto BBC/Getty Images
Image caption DaraktaVicky Featherstone (daga hagu) da kuma marubuciya Abi Morgan sun taimaka wajen shirya wasan

"Amma tambayarka a wurina ita ce, kana ganin duniya za ta fi samun ci gaba idan da a ce mata zalla ne suke mulkinta?

"A wani lokaci, ba daya ba ne. Maza ne suke mulkin duniya. Kuma ina tunanin duniya za ta fi samun ci gaba idan da mata suna mulkin ta ne.

"Za a samu raguwar yake-yake. Za a samu raguwar sayar da makamai. Za a samu raguwar al'amura da dama. Za mu fi inganta abubuwa a duniya. Al'amura za su daidaita fiye da yadda suke yanzu. Shakka babu."

'Ko mace tana tunani daban da yadda maza suke yi?'

Za a ci gaba da neman amsar wannan tambayar a cikin kwana hudu a tsakanin taurari biyar da za su tattauna a tsakaninsu, wadanda suke shugabantar hukumomi kama daga shige-da-fice da tattalin arziki da kuma harkokin makaman nukiliya.

Taurarin za su bayyana wa masana manyan matsalolin da duniya ke fuskanta. Akwai shiri kai-tseye, kuma shirin ranar Asabar da za a wasa shi ne ta kafar yada labarai ta BBC.

Marubuciya Abi Morgan, wacce ta rubuta labarin fim din Iron Lady, da Suffragette, da sauransu, na daga cikin taurarin da za su taka rawa a shirin.

Hakkin mallakar hoto Donald Christie
Image caption Yael Bartana ce ta kirkiri shirin kuma zai ta fito a cikin shirin

Shirin zai samu bakuncin jarumin fim din Dokta Strangelove na shekarar 1964, wato Peter Sellers. Ko kuma fim din "How I Learned to Stop Worrying and Love the Bomb" wanda shi ne babbar tattaunawa da manyan shugabanni maza suka yi kan yadda za su sake gina duniya bayan da makamin Nukila ya wargaza duniya a Yakin Duniya na Biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mata kalilan ne suka halarci taron kungiyar tsaro ta NATO wanda aka yi a watan Mayun da ya wuce

"Da gaske ne idan aka waiwayi baya wato shekaru 10,000 da suka gabata tun lokacin juyin-juya-halin harkar noma, ba a taba samun wani lokaci da mata suka samu rinjaye a madafun iko," in ji Bartana.

Tana kokarin kawo wani abu sabo ne.

Ba wai kawai samun mata da yawa a madafun iko ba kamar siyasa da harkokin addini da kasuwanci da al'adu da aikin soji da na jarida ba - amma har da kara sake dadadden tunaninmu dangane da maza da mata da yara da 'yan mata da kuma damar da suke da ita.

Yadda muke tallata bajintar mata —Gbemi

Mata na fuskantar cin zarafi a majalisu

'Shugaba Buhari ya dauki mata da daraja'

'Za a iya samun babban sauyi'

Ta ce ta dade tana ta fafutika da tunanin cewa ko duniya za ta samu ci gaba fiye wanda ake da shi yanzu idan mata suka samu madafun iko?

"Tambaya ce da ba zan iya amsawa ba. Zan iya cewa na yi amanna cewa duniya za ta fi haka ci gaba, amma ba mamaki a kara maimaita matsalolin ko kuma a kasa magance su.

"Amma kuma dai a lokaci guda, ina cewa ba a bai wa mata dama a wurare da yawa ba a duniya. Don haka a dan ba su dama."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akwai abubuwa da dama da suke haifar da wariya da cin hanci a duniya

Ta kuma bayyana cewa ba kowacce matsala ba ce a duniya a za dora alhakin aukuwarta kan matsalar danniyar da maza sukai wa mata.

"Akwai abubuwa da dama da suke haifar da wariya da cin hanci da rashin daidaito a wurare da dama a matakai daban-danan."

"Amma dai zan iya amanna cewa idan mata suka samu madafun iko da dama, watakila, watakila a samu babban sauyi. Ina so na samu yakinin kan hakan."

Labarai masu alaka