Nigeria: 'An zuzuta rikicin kabilanci na Calabar'

Map of Nigeria

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa an kashe mutane fiye da 100 a sanadiyar wani rikici da ya barke tsakanin wasu al'umomi makwabta a jihar Kuros Riba da ke Kudancin kasar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kuros Riba, Muhammad Hafiz Inuwa, ya ce mutum daya ne kawai ya rasa ransa a sakamakon rikicin.

"Magana ta gaskiya ita ce mutum daya ne muka sami rahoton mutuwarsa, in ji shi."

Kwamishinan ya bayyana cewa mutum biyu kuma ba a gansu ba, "Mutum biyu kuma aka ce an sace su, anyi gaba da su - wadanda har yanzu muna nemansu."

Al'ummomin Wanikade da na Wanihem da ke karamar hukumar Yala sun shafe kwanaki uku suna karawa da juna sabili da rikicin wasu gonaki.

Kuma ya ce babu gaskiya a rahotannin da ke cewa an kona dubban gidaje, inda yace muhallan da ke al'umomin ba su wuce guda 500 ba.

"Kuma dangane da cewar mutum 150 sun rasa rayukansu, ai ba ma zai yiwu ba."

Ya kuma tuhumi wadanda ya kira masu "Yada jita-jita domin son ran su, watakila domin su kara haddasa wata fitinar dabam".

Amma a jiya shugaban hukumar bayar da taimakon gaggawa ta jihar Kuros Riba, Mista John Inaku ya tabbatar da faruwar rikicin.

A halin yanzu, mutanen da rikicin ya rutsa da su suna gudun hijira a karamar hukumar Oju da ke makwabciyar jihar Binuwai.

Labarai masu alaka