Jami'ar Northwest ta Kano ta zama Yusuf Maitama Sule University

Kano State's Northwest University
Image caption Jami'ar Northwest University wacce gwamnatin jihar Kano ta canza wa suna zuwa Yusuf Maitama Sule University a Kano

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta sauya sunan jami'ar Northwest da ke birnin Kano zuwa Yusuf Maitama Sule University, domin karrama marigayi Dan Masanin Kano wanda ya rasu a ranar Litinin.

Gwamnatin ta kuma sauya sunan titin Dawaki Road, inda gidan marigayin yake, zuwa Yusuf Maitama Sule Road.

Shi kuwa titin Yusuf Maitama Sule Link Road yanzu ya koma Jafaru Dan Mallam Link Road.

Majalisar zartaswar jihar ce ta dauki wadannan matakan bayan wani taro na musamman da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya jagoranta ranar Laraba da daddare.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce ta dauki wadannan matakan ne "Domin karrama marigayi Dan Masanin Kanon saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Kano da arewacin Najeriya har da Najeriya gaba daya."

Gwamnatin ta ce ta yi la'akari da "irin kiraye-kirayen da jama'a suka yi" daga sassa daban-daban na kasar ga gwamnatin domin ta karrama marigayi Dan Masanin Kano.

A ranar Litinin e ALlah ya yi wa Dan Masanin Kano rasuwa bayan gajeriyar rashin lafiya a kasar Masar.

An kuma yi jana'izarsa a ranar Talata a kofar fadar Kano.

Labarai masu alaka