Biafra: Hanyoyi 5 da yakin basasa ya sauya Nigeria

Four starving Biafran children sit and lay around a bowl of food in the dirt during the Biafran war Hakkin mallakar hoto Hulton Archive
Image caption Kimanin mutane miliyan 1 zuwa miliyan 2 suka mutu dalilin yakin Biafra

Bayan shekara 50, har yanzu ana ganin tasirin yakin basasar Najeriya na Biafra a cikin kasar har da ma a nahiyar Afirka.

Kallon-kallo

Yakin ya biyo bayan juyin mulkin watan Janairun shekarar 1966, inda aka kashe yawancin shugabannin kasar - ciki har da firai ministan farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa - da wasu manyan hafsoshin sojoji.

Wasu sojoji masu bore ne suka yi juyin mulkin, wadanda yawancinsu daga kabilar Igbo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya suka fito.

Wannan ya janyo tashin hankalin sauran mutanen sassan arewaci da yammacin kasar, wadanda suka mayar da martani a kan kabilar Igbo.

Da ya ga abin da ke faruwa ga 'yan uwansa 'yan kabilar Igbo, sai wani kanar na rudunar sojin Najeriya, Emeka Ojukwu, ya yi shelar kafa kasar Biafra - abin da gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da shi. Mutane fiye da muliyan daya ne suka mutu a yakin basasar da aka yi.

Zuwa yau, akwai sauran rashin yarda tsakanin yawancin kabilun Najeriya - kuma babu wani dan kabilar Igbo da ya mulki kasar bayan yakin basasar.

Biafra ta dare

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kanar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu wanda ya jagoranci jamhuriyar Biafra

Yunkurin ballewar da Igbo suka yi ya sake kunno kai a 'yan shekarun nan - watakila ma na yanzu ya fi irin na baya sosai.

Shugaban wannan sabon yunkurin na ballewa kuma mai rike da fasfon Birtaniya da Najeriya, Nnamdi Kanu - wanda a ka bayar da belinsa bayan ya shafe fiye da shekara guda a tsare sabili da tuhumarsa da hukumomi ke yi da laifukan sa suka shafi cin amanar kasa - ya ce: "Ko dai Biafra ko mutuwa; dole daya cikin biyun nan ta faru."

Ya fada wa BBC cewa, "ci gaban al'umomi, da ci gaban tattalin arziki, da samar da yanayin jin dadin jama'a ba su yiwuwa saboda akwai rashin yarda, da kiyayya tsakanin mutanen kasar - saboda haka abu mafi kyau shi ne mu rabu da juna."

Amma ba duka 'yan kabilar Igbo ke mara wa yunkurin ballewar yankinsu daga Najeriya baya ba.

A watan Yuni, wasu manya na yankin Igbo da suka hada da 'yan siyasa da masu rike da mukaman gargajiya sun fito karara suna nesanta kansu daga yunkurin kafa kasar ta Biafra - amma sun yi kira da a sake fasalin kasar ta fannonin mulki da raba albarkatun kasa.

Jiya ba yau ba

Hakkin mallakar hoto STEFAN HEUNIS
Image caption Najeriya na bikin zagayowar yakin Biafra tun watan Mayun bana

Koke-koken danniya da rashin da damawa da al'uma a fagen siyasa, ba kabilar Igbo kawai ke yi ba.

Alkaluman bincike daga kungiyoyin kasa da kasa da dama sun tabbatar da yankin arewacin Najeriya shi ne yankin da yafi ko wanne yanki talauci.

A halin yanzu, Najeriya na da jihohi 36 da gwamnatin tarayya mai karfin iko, a maimakon larduna uku masu karfi da gwamnatin tsakiya maras karfi sosai.

A fili ta ke cewa Najeriyar shekarun 1960 ba irin ta yau ba ce. Adadin al'umar kasar ya ninka fiye da sau uku kuma albarkatun kasar sun habaka matuka, yadda kasar yanzu ita ce ta shida a jerin kasashe masu fitar da danyen man fetur a duniya.

To amma galibin makudan kudaden da kasar ke samu daga arzikin man fetur na zurarewa kana akan wawure su ta hanyoyin cin hanci da rashawa, lamarin da ke barin yawancin mutanen kasar cikin halin talauci da kuncin rayuwa.

Masu kula da al'amura sun ce shekaru da dama da aka kwashe gwamnati na yin watsi da batun kyautata rayuwar al'uma, sun sanya bacin rai da kunci da fushi a zukatan matasan Najeriya, da kuma sanyaya masu gwiwa game da makomar rayuwarsu, lamarin da ya kara samar da yanayi na saurin samun tashin hankali.

Kalubalen Tsaro

Hakkin mallakar hoto EMMANUEL BRAUN
Image caption Najeriya na fuskantar kalubale daga sassa daban-daban na kasar.

Najeriya na fuskantar kalubalen batutuwan tsaro a shekarun baya-bayan nan.

Duk da cewa hukumomin sojin kasar na samun nasarori a yaki da kungiyar Boko Haram a arewacin kasar, amma har yanzu ba a iya dakile ta baki daya ba.

Yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur shi ma har na fuskantar tashin hankali daga loakci zuwa lokaci, idan aka hada da matsalar ta yunkurin samar da kasar Biafra, za a iya cewa yanzu Nijeriya na da taura uku a bakinta

Wadanda suke son Najeriya ta rabe suna ta kiraye-kirayen a yi zaben raba gardama - kiraye-kirayen da hukumomin kasar da sarakunan gargajiya ba su amince da su ba, suna masu cewa hadin kan Najeriya ya fi gaban wargi.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce jami'an tsaron Najeriya sun kashe a kalla mutum 150 tun watan Agusta 2015 a kokarin dakile zanga-zangar neman kafa kasar Biafra, zargin da hukumomin soji da na 'yan sanda suka musanta.

Wa'adi ga Igbo mazauna arewa

Hakkin mallakar hoto SIA KAMBOU
Image caption Masu fafutukar neman kasar Biafra sun kara kaimi

A karon farko, wasu kungiyoyin matasa a yankin arewacin Najeriya su ma sun shiga sahun masu kiraye-kirayen a raba kasar wadda ita ce kasa mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Hadaddiyar Kungiyar Matasan Arewa ta bai wa 'yan kabilar Igbo wa'adin nan da 1 ga watan Oktoban 2017 su fice daga yankin na arewa ko idan ba haka ba a tursasa masu ficewa.

'yan kabilar Igbo wacce a ke ganin tafi kowace kabila warwatsuwa a Najeriya, sun fi yawa a yankin kudu maso gabashin kasar. Suna kokun ana maida su saniyar ware a harkokin kasar, idan aka kwatanta su da kabilun Hausawa da Yarabawa.

Kiraye-kirayen a raba Najeriya dai na kara amo, matsin lamba na karuwa a kan gwamnati, kana zaman tankiya tsakanin al'umomin Najeriya na dada zafafa.

Amma idan ka tambayi yawancin 'yan Najeriya, za su ce ba sa son a kara yin yakin basasa kwatankwacin wanda kasar ta fuskanta a shekarun 1960.

Wasu masu lura da al'ummaran yau da kullum suna cewa karin tattaunawa da shugabanci na-gari, da kuma kamanta adalci wajen rabon dimbin albarkatun kasar za su taimaka wajen rage zaman tankiya tsakanin al'umomin Najeriya, da zullumi, kana rayuwar jama'a ta inganta.