'A haramta amfani da 'yar tsana mai siffar yara don jima'i'

ba a san yawan adadin mutum-mutumin da aka sayar ba
Image caption ba a san yawan adadin mutum-mutumin da aka sayar ba

Mawallafin wani rahoto ya yi kira da a haramta shigar da 'yar tsanar mai siffar yara wadanda a ka yi musamman don yin jima'i.

Farfesa Noel Sharkey ya ce, akwai bukatar al'umma su san illar jima'i da mutum-mutumi.

Gidauniyarsa ta Responsible Robotics ta gudanar da wani bincike a kan wannan batu.

Farfesa Sharkey ya ce a halin yanzu kamfanoni kadan ne kawai ke kera mutum-mutumi domin jima'i.

Ya kara da cewa juyin-juya halin da ke zuwa na mutum-mutumin zai kawo sauyi a kan hakan.

Rahoton mai sunan "Our Sexual Future With Robots", watau makomar jima'i da mutum-mutumi, an rubuta shi ne don a jawo hankali a kan batun.

Binciken ya tabbatar da cewa abu ne mai wahala a gano adadin mutanen da suka mallaki irin wadannan mutum-mutumin, saboda kamfanonin da ke kera su ba ya bayyana adadinsu.

Sai dai Farfesa Sharkey ya ce, lokaci ya yi da jama'a za su farka da sanin akwai makomar jima'i tsakanin mutum-mutumi da mutane na gaba.

"Muna bukatar aiwatar da manufofi da za su sa ido a kai da kuma wayar da kan jama'a don yin shawara a kan abin da yake amintacce ne ko a'a, in ji shi.

Ya kara da cewa, a matsayinmu na al'umma muna bukatar mu yi tunanin abun da za mu yi game da shi. Ni ma ban san amsoshin ba, kawai dai ina tambayar ne.

Kamfanonin da suke kera mutum-mutumin jima'i sun hada da Android Love Doll, da Sex Bot da kuma True Companion. A yanzu sun fara kera wanda zai iya motsi da magana.

Tuni kamfanin ya saki manhajar, wanda ya bai wa masu amfani da shi damar shirya da kuma muryoyin 'yar tsanar.

A yanzu ana samun 'yar tsanar jima'i da take kama da yara, wadda yanzu haka wata kotu a Canada na yin nazari a kan cewa ko mallakarta ya saba doka.

Wani mazaunin Newfoundland Kenneth Harrison ya bayar da odar 'yar tsana daga Japan wadda ake kira da samfurin Harumi.

Image caption Wata mace ta rungume mutum-mutumi

Rahoton ya yi nazari a kan yanayin dangantakar mutum-mutumi, sai dai abin tambaya a nan shi ne, ko mata na son jima'i da namijin mutum-mutumi?

Wata masaniyar halayyar mutum-mutumi a jami'ar De Montfort, Dakta Kathleen Richardson, ta amince da rahoton marubutan da yake cewa za a haramta jima'in mutum-mutumin yara.

Ta ce, " A zahirin gaskiya ba 'yar tsanar ba ce matsala, babbar matsalar ita ce yadda ake cinikin abun. Jima'in mutum-mutumi wani sabon salon batsa ne".

Tana da yakinin cewa, irin wadannan mutum-mutumi abu ne da ba za a iya hanawa ba, kuma yana kara jawo kauracewa jama'a."

Farfesa Sharkey ya ce, yanzu haka akwai rashin dacewa tsakanin wadanda suke sayar da irin wadannan mutum-mutumi suna bukatar masu sayan kayansu su samu yakine game da 'yar tsanar da kuma zahirin abin da suka mika.

Ya ce, "Ba zan iya kallonsu a matsayin mutane ba har zuwa shekara 50 masu zuwa. Ko da yaushe suna zama kamar wani karamin abin tsoro, kuma dabarun yin maganarsu yanzu sun zama abin tsoro.

Har ila yau, dakta Richardson ta yi tambaya ko irin wadannan mutum-mutumi za su zama wani abu na al'ada, ko wani abu da zai iya yiyuwa ta fuskar fasaha.

"Rahoton na ganin cewa kana iya kirkiro mutum-mutumin da yake motsi da zai iya yin martani ga mutane, sai dai a cikin wannan al'amari abu ne mai wahalar yarda," in ji ta.

Image caption Hoton mutum-mutumi

Labarai masu alaka