Nigeria: Kotu ta yi watsi da karar 'yan Shi'a

Zakzaky Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan shi'a sun dade suna zanga-zagnar neman a saki jagoran kungiyar tasu

Wata Kotun tarraya a jihar Kadunan Najeriya ta yi watsi da karar da jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya shigar kan sojin kasar.

Zakzaky ya shigar da karar ne domin neman diyya bayan soji sun kashe daruruwan mabiyansa tare da lalace kadarorinsa a watan Disambar shekarar 2015.

Sai dai alkalin kotun, Mai Shari'a Salisu Sha'aibu, ya ce kotun ta yi wasti da karar ne saboda ba ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka shigar ba.

Sannan ya ce mabiya Shi'ar da shugabansu sun rarraba karar a kotrunan kasar da dama. Amma ya ce za su iya daukaka kara.

Amma lauyan Sheikh Zakzaky, Haruna Magashi, ya ce bai gamsu da hukuncin da alkalin ya yanke ba, yana mai cewa ra'ayin mai shari'ar ne kawai, kuma bangarensa zai yi nazari domin sanin irin matakin da zai dauka.

Kimanin 'yan Shia 349 sojoji suka kashe a rikicin bayan da suka zarge su da yunkurin kisan Hafsan sojin kasa Laftanar Janar Tukur Buratai.

Sai dai mabiya kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmi wadanda ke goyon bayan Iran, sun yi watsi da zargin, suna masu cewa kage ne kawai. Sannan suka ce adadin wadanda aka kashe ya kai 1000.

Yadda aka kama Zazaky

A watan Disambar Shekarar 2015 ne sojoji suka kai samame gidan Sheikh Ibraheem Zazaky bayan wasu mabiyansa sun katse hanyar da hafsan sojin Najeriya, Leftanar-Janaral Tukur Buratai yake bi.

Bidiyon da rundunar sojin Najeriya ta fitar ya nuna yadda jami'an soji suke rokon mabiya Zakzaky su ba shi hanya amman ba su yarda ba, suna masu cewar sai sojojin sun kira shugabansu.

Daga bisani sai bidiyon ya nuna yadda ayarin Tukur Buratai yake wucewa ba tare da nuna yadda aka sama masa hanyar ba.

Daga bayan su 'yan Shi'an sun fitar da wani bidiyon inda suka nuna yadda sojoji suka ja daga a kusa da cibiyar Husainiyya ta 'yan Shi'a, inda suka ce daman an shirya a far musu ne.

Bayan an kai harin dai, hukumomin Najeriya sun kama Sheikh Zakzaky da matarsa, lamarin da ya sa mabiyansa suka yi ta zanga-zanga a wasu biranen kasar.

Kasar Iran, wacce ke goya musu baya, ta nemi a sake shi.

Ita gwamantin Najeriya dai ta ce ba za ta saki Zakzaky ba domin ta daukaka kara kan hukuncin da ya ce ta yi hakan.


Yadda Shia ta ke a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
  • 'Yan Shi'a tsiraru ne a Najeriya, amma rahotanni na nuna cewa yawansu na karuwa
  • Kungiyar IMN, wadda aka kafa a shekarun 1980, ita ce babbar kungiyar 'yan Shi'a wadda Ibraheem Zakzaky ke jagoranta
  • Tana gudanar da makarantu da asibitocinta a wasu jihohin arewacin kasar
  • Kungiyar tana da tarihin arangama da jami'an tsaro
  • IMN tana samun goyon bayan Iran inda 'yan Shi'a suke da rinjaye, kuma 'yan kungiyar na yawan zuwa Iran karatu
  • Kungiyar Boko Haram da ke ikirarin bin mazhabin Sunna tana kallon 'yan Shi'a a matsayin fandararru, kuma ta sha kai musu hari

Ga rahoton da Nura Mohammed Ringim ya turo mana daga Kaduna :

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kotun ta yi watsi da karar ne saboda rashin gamsuwa da hujjoji da kuma rarraba kara