Rahama Sadau za ta gana da Priyanka Chopra ta India

Rahama Sadau
Image caption Rahama Sadau ta ce burinta shi ne a fito a fina-finan Hollywood, Bollywood, Nollywood, da kuma Kannywood

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Rahama Sadau ta ce tana shirin ganawa da takwararta ta Bollywood Priyanka Chopra nan ba da dadewa ba.

Jarumar ta shaida wa BBC cewa Priyanka ce jarumar da ta sanya mata sha'awar kallon fina-finai da ma shiga harkokin fim.

Hasalima, wasu suna kiranta da suna Priyanka.

Rahama ta kara da cewa wannan shi ne karo na uku da ta tattauna da Priyanka a shafukan sada zumunta kuma tana matukar jin dadi.

"Na soma magana da ita a Twitter a 2013, sannan muka sake magana a 2015 amma maganar da muka yi a jiya (Laraba) ita tafi farantan rai. Da na nuna yadda nake kaunarta, ita kuma ta yaba min sannan ta ce tana fata za mu sadu nan ba da dadewa ba", in ji Rahama Sadau.

Hakkin mallakar hoto INSTAGRAM
Image caption Rahama ta soma kaunar Priyanka tun tana karamar yarinya

Jarumar ta shaida wa Nasidi Adamu Yahaya cewa tuni ta soma tattaunawa da makusantan Priyanka Chopra kuma a shirye take ta gana da ita domin tattaunawa kan batutuwa da dama.

A cewarta, "Priyanka Chopra mace ce mai kamar maza; tana da jajircewa da fuskantar kowanne irin kalubale. Haka kuma mace ce wacce idan ta sanya wani abu a gabanta ba ta juyawa baya. Shi ya sa nake koyi da ita".

Wannan dai ba shi ne karon farko da Rahama Sadau ke shirin ganawa da manyan jaruman fina-finai ba; ko da a shekarar 2016 ta je Amurka bisa gayyatar fitaccen jarumin nan kuma mawakin Hollywood, Akon.

Akon ya gayyace ta Amurka ne bayan rikicin da dakatar da ita daga Kannywood ya janyo.

An kori jarumar ne saboda "ta rungumi" wani mawaki a cikin bidiyon wakar da ya yi, ko da yake daga bisani ta bai wa magoya bayanta hakuri kan batun.

Labarai masu alaka