Babu wanda ya isa ya cire Magu — Osinbajo

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce 'yan majalisar dattawan kasar ba su isa su cire shugaban riko na EFCC Ibrahim Magu daga mukaminsa ba.

Farfesa Osinbajo ya bayyana haka ne a Kaduna ranar Alhamis, lokacin bude reshen ofishin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati, EFCC na jihar.

Mukaddashin shugaban kasar, wanda Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya wakilta, na yin raddi ne ga 'yan majalisar dattawan, wadanda suka nemi a sauke shugaban na EFCC.

"Magu na yin aikin da ya kamata, kuma ya zama dodo ga masu aikata cin hanci da rashawa," in ji Osinbajo.

Ya kara da cewa "idan dai har ina nan a matsayin mukaddashin shugaban kasa kuma Shugaba Buhari na kan mulki, to babu wanda ya isa ya cire Magu".

A ranar Talata ne sanatocin suka yanke shawarar cewa ba za su tantance duk wani mutum da Mista Osinbajo ya mika musu domin tabbatar musu wasu mukamai ba har sai an sauke Mista Magu.

Wasu na ganin wadannan kalamai za su kara rura wutar rikicin da ke tsakanin bangaren shugaban kasa da kuma na 'yan majalisa.

An dade ana kai ruwa rana tsakanin bangaren zartarwa da na 'yan majalisar a kan shugaban rikon na EFCC.

Majalisar dai ta ce ba za ta amince a tabbatar da Ibrahim Magu kan mukaminsa ba saboda zarge-zargen da ake yi masa na aikata ba daidai ba.

Sai dai ya sha musanta zarge-zargen.

Kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga bangaren 'yan majalisar.