'Snapchat na sanya rayuwar yara cikin hadari'

Tap ghost mode on phone

Makarantu na gargadin iyayen yara cewa sabon shafin sadarwa na Snapchat wanda ke nuna hakikanin wurin da mutum yake ka iya sanya rayuwar yara cikin hadari.

Snapchat dai na bayar da dama ga masu amfani da shi da su bayyana hakikanin wurin da suke ga masu bibiyarsu.

A wata wasika da BBC ta gani, wata makaranta ta ce shafin na kawo "babbar matsala ga kariyar mutane" saboda za a iya bibiyar yaran ta hanyar amfani taswirar shafin.

Sai dai kamfanin na Snapchat, wanda ke tafiyar da shafin, ya ce kunna manhajar ake yi, kuma za a iya rufe ta a ko wanne lokaci.

Mene ne taswirar Snapchar (Snap Map)?

An kaddamar da shafin Snap Map ranar 21 ga watan Yuni wanda zai bayar da dama ga mutane su binciko bangaren da suke da hotuna da bidiyoyin da aka wallafa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli wannan bidiyon don sanin me Snapchat ke yi

Kuma tana bayar da dama ga mutane da su bayyana hakikanin wuri da suke da wurin da mutane (abokai), da suke mu'amala da su a shafin.

Wadanda suka bayyana wurin da suke a shafin za a gansu a cikin taswirar kamar wani fim din ban dariya na yara (cartoon).

Su wa abin zai dama?

Wasu makarantun na fargabar cewa nuna hakikanin inda mutum yake a shafin wata babbar barazana ce, tare da gargadin cewa za a iya amfani da shi wajen gano adireshin gidan mutum, da hanyoyin da yake bi wajen tafiye-tafiyensa, da makarantun da kuma wuraren ayyukan mutanen.

Yayin da kake wallafa bayananka a shafin ga abokanka, wannan zai hada har da mutanen da ba ka sansu ba, kamar abokan da ka hadu da su ta wasu manhajojin da wasu shafuka na intanet.

Wasu na sukar hanyar da aka bi aka dora taswirar a Snapchat ba tare da yin bayanin cikakkaiyar hanyar da take aiki ba.

"Mun sani kamfanonin fasaha na kirkirar sababbin hanyoyin da suke inganta manhajojinsu, amma muna karfafa musu gwiwa da su samar da cikakken bayanai game da iyaye da kuma kananan yara, saboda su san yadda za su kare kansu," inji Rose Bray.

"Ya kamata a yi wa iyaye wani gargadi, don su duba bayanan kafin su yadda yaransu su fara amfani da su"

Image caption Paula ta damu kan cewa danta ya kan kunna wajen da ake gane inda mutum yake

Me manhajar Snapchat din ke cewa?

A wata sanarwa, shafin na Snapchat ya ce: "kariya al'umarmu na da matukar muhimmanci a garemu, muna son tabbatar wa da masu amfani da shafin, da iyaye, da masu ilimi na da bayanan sirri game da yadda shafin ke aiki".

Kamfanin na nuna cewa bayyana wurin da mutum yake a shafin ainihi a kashe take, kunnata ake yi kuma za a iya kasheta a kowanne lokaci.

Kamfanin ya shaida wa BBC cewa shafin na kare bayanan sirri, saboda haka abokai za su iya amfani da shi domin samo mutumin da za su yi abota da shi.

Ya kara da cewa: "mafiya yawan hulda da ake yi a shafin na Snapchart a kan yi shi tsakanin makusantan abokai", ba kamar sauran shafukan sada zumunta wadanda aka yi su don mutane su samo sabbin abokai da ba su sani ba.

To sai dai da BBC ta tambayi kamfanin cewa me yasa ba sa gargadin masu amfani da shi ba? Sai kamfanin ya ki cewa uffan a kai.

Ta yaya za ka tsaida amfani da Snap Map?

BBC ta bayyana wannan 'yar gajeriyar hanya, don taimakawa wajen yadda za a daina amfani da shi, wanda zai bayyana wa mutane yadda za su kashe manhajar da ke nuna inda suke.

  • Idan wayar na son daukar hoto, ka latsa fuskar domin bude taswirar Snap.
Hakkin mallakar hoto Newsround
Image caption Latsa fuskar wayar domin bude taswirar Snap
  • Ka taba saitin da ke hannun dama a fuskar wayar (screen )
Image caption • Ka taba saitin dake hannun dama a fuskar wayar (screen )
  • Ka taba makunnar domin kashe wurin da da ake aika sako
Image caption • Ka taba makunnar domin kashe wurin da dake

Labarai masu alaka

Karin bayani