Dakarun Nijar sun kashe fararen hula 14 kan kuskure

Sojojin Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin Nijar sun kashe fararen hula 14 bisa kuskure

Dakarun sojin jamhuriyar Nijar dake sintiri a yankin Bosso sun kashe fararen hula 14 da suke zaton 'yan bindiga na kungiyar Boko Haram a kudu maso gabashin kasar.

Fararen hula , wadanda duk manoma ne , sun kasance a warin da aka haranta a kusa da kauyen Abadam, kan iyakar kasar da Najeriya.

Biyu daga cikin su 'yan Nijar ne kuma sauran 'yan Najeriya.

Sai dai , yan uwan mamatan na cewa aikin gangan ne . Amma hukumomin yankin na cewa kuskure ne sojin sukayi.

Har yanzu ba a bayyana yadda abubuwa suka faru ba kuma me ya kar fararen hular wurin.

Kungiyar Boki Haram na Najeriya amma su kan kai hare-hare a wasu kasashe.

Dubban mutane a yakin kudu maso gabashin Diffa sun rara muhallansu kuma an hana fararen hulla zuwa wurare da dama.

Amma yawancinsu na dawowa domin kula da gonakinsu.

An dai samu bambamcin a cikin rahotanni game da sojojin da suka kai harin.

Kamfanin dillacin labaran na AFP ya ruwaito cewa ta hanyan harin iska aka kashe mutane bayan da suka dawowa daga kulawa da gonakinsu. Amma Reuters kuma ya ce sojojin da sintiri yankin ne suka yi harbin wuta da ya kaashe mutanen.

Labarai masu alaka