An dakatar da shugaban NHIS na Nigeria kan zargin cin hanci

Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Najeriya NHIS Usman Yusuf Hakkin mallakar hoto Concise News]
Image caption Usman Yusuf ya musanta zargin da ake yi masa

Ministan Lafiya na Najeriya Isaac Adewale ya bayar da umarnin dakatar da shugaban hukumar kula da inshorar lafiya na kasar (NHIS), Usman Yusuf, bisa zargin da ake masa na wawure kudin hukumar.

Wani kwamitin Majalisar Dattawan kasar ne yake zargin Mista Yusuf da yin sama da fadi da dubban dalolin hukumar.

Ko da yake dai a wata hira da Mista Yusuf ya yi da BBC Hausa a baya-bayan nan ya musanta zargin da ake masa.

Mai magana da yawun ma'aikatar lafiyar Mrs Akintola shaida wa BBC cewa an dakatar da shi ne na tsawon wata uku kafin a kammala bincike a kan zarge-zargen da ake yi masa.

Ta ce a ranar Alhamis ne ministan lafiya na Najeriya Isaac Adewole, ya bayar da umarnin a dakatar da shugaban NHIS din ba tare da bata lokaci ba.

Ta kara da cewa ana tuhumarsa, "a kan abubuwa daban-daban, amma ba zan iya tabbatar da ko akwai batun kudin hukumar ba" kamar yadda rahotanni suka nuna.

Majalisar Dattawan na tuhumar Mista Yusuf ne da kashe kudaden hukumar har kimanin naira miliyan 292 ba bisa ka'ida ba.

Mista Yusuf ya zama shugaban hukumar NHIS ne a watan Yulin shekarar 2016.

Sai dai zuwa yanzu ba a ji ta bakin Mista Yusuf ba kan wannan dakatarwa da aka yi masa.

Labarai masu alaka