Ashe ba a dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood ba?

  • Nasidi Adamu Yahya
  • BBC Hausa
Bayanan bidiyo,

Ba wanda ya dakatar da ni- Rahama Sadau

Rahama Sadau. Da zarar an ambaci wannan suna babu abin da zai fado ran mutane sai ce-ce-ku-ce saboda kurar da mai sunan ta tayar a shekarar 2016 lokacin da aka nuna ta a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.

Wannan batu dai ya jawo hankalin duniya musamman saboda caccakar da aka rika yi wa jarumar ta fina-finan Kannywood, abin da ya kai ga "korarta" daga yin fina-finan na Hausa.

Sai dai a zahiri Rahama Sadau, wacce ta soma taka rawa a fina-finan Kannywood a shekarar 2013, mace ce mai kamar maza, kamar yadda a duk lokacin da muka hadu take gaya min.

"Ni fa mace ce jaruma wadda idan na sa abu a gaba sai na kammala shi domin babu abin da ke dakatar da ni daga son cika burina".

Bayanan hoto,

Rahama Sadau ta ce tana so ta taka rawa a dukkan rukunan fina-finan duniya

Mene ne burinta?

A wata hira ta musamman da na yi da ita a shekarar 2015, jarumar ta shaida min cewa "babban burina shi ne na taka rawa a matsayin jaruma a dukkan manyan bangarorin fina-finan da ake yi a duniya: Hollywood, Bollyywood, Kannywood da kuma Nollywood".

Ta kuma jaddada min shaukinta na cika wannan buri nata a tattaunawar da muka yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Tun da ta soma fitowa a fina-finan Kannywood take hankoron baza komarta kuma tun ma kafin a "kore" ta daga Kannywood ta soma fitowa a fina-finan Nollywood da ake yi a kudancin Najeriya.

Sai dai babu ko shakka hanawar da aka yi mata fitowa a fina-finan Kannywood ta zamar mata tamkar gobarar Titi a Jos.

Jim kadan bayan haka ne fitaccen mawakin nan kuma jarumin fina-finan Hollywood Akon ya gayyace ta birnin Los Angeles na Amurka domin share mata hawaye.

A can ne kuma ta fito a wani fim din Hollywood wanda shi Akon din ya bayar da umarnin hadawa.

"Na ji dadin zuwa Amurka domin kuwa na koyi abubuwa da dama a kan fina-finai. Na yi fitowa ta musamman a wani fim da Akon ya hada. Yanzu kuma ina shirin fitowa a wasu fina-finan na Hollywood. Hasalima jiya-jiyan nan wasu Amurkawa suka zo nan Najeriya inda za mu ci gaba da daukar wani fim", in ji tauraruwar.

'Babu wanda ya dakatar da ni'

Da yake Rahama Sadau na cikin jaruman da suka fito a fim din na Rariya, na tambaye ta ko an janye korar da aka yi mata daga Kannywood, sai dai ta ce dama can ba a kore ta ba.

"Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood. Har yanzun nan babu wanda ya aiko min da wata takarda da ke nuna cewa an sallame ni daga Kannywood.

An rage ganina a fina-finan ne saboda, kamar yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan Nollywood da kuma gudanar da sauran al'amuran rayuwata.

Amma yanzu zan koma yin fina-finan na Hausa gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da fim dina na Rariya ya yi. Zan ci gaba da daukar nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba da yi", in ji jarumar.

Na fahimci cewa akwai wata fahimtar juna a tsakanin kungiyar MOPPAN da ke sa ido kan masu shirya fina-finan Kannywood da Rahama Sadau ta yadda za ta janye jikinta daga fitowa daga fina-finan na Hausa, alabashi su kuma su bar ta ta koma fita a fina-finan bayan wani lokaci, musamman idan mutane suka soma mantawa da abubuwan da suka faru.

Da na tambaye ta kan ko ta yi da-na-sanin fitowa a bidiyon wakar da ya janyo ce-ce-ku-ce, Rahama Sadau ta yi murmushi sannan ta ce "kar ka manta na bai wa magoya bayana hakuri saboda abin da ya faru. Amma daga haka ba zan sake cewa komai ba".

Ganawa da Priyanka Chopra

Ita dai Rahama Sadau, wacce ke "jin" yaren Hindu kamar Amitabh Bachchan, ta shaida min cewa ta soma sha'awar fitowa a fina-finai ne saboda kaunar da take yi wa fittacciyar jarumar Bollywood, Priyanka Chopra.

"Tun ina karamar yarinya nake kallon fina-finan India kuma su ne ma suka yi gagarumin tasiri a rayuwata. Watakila hakan ba zai rasa nasaba da son fina-finan na India da mahaifina ke yi ba: ya je kasar India tun muna yara kuma shi ne ya soma koya min Indiyanci. Amma a dukkan jaruman fina-finan India babu wadda na fi kauna kamar Priyanka Chopra: mace ce jaruma, hazika kuma kuli-kuli ce mai sa gabanta inda take so," in ji jarumar.

Rahama Sadau ta ce takan yi wa Priyanka Chopra magana a shafukan sada zumunta akai-akai domin bayyana mata irin kaunar da take yi mata.

Bayanan hoto,

Rahama Sadau ta ce tana so ta taka rawa a dukkan rukunan fina-finan duniya

"Karon farko da na yi mata magana a Twitter shi ne a 2013, sai kuma a 2015 da kuma shekaranjiya [Talata]. A karon farko ba ta ce min komai ba; a karo na biyu kuma ta tambaye ni ni wace ce sai na gaya mata cewa ni jarumar fina-finan Hausa ce da ke matukar kaunarta.

Amma shekaranjiya da na yabi wani abu da ta wallafa a Twitter sai kawai ta ce min ta gode kuma tana fatan za mu hadu nan ba da dadewa ba. Hakan ya sa na ji dadi sosai", a cewar Sadau.

Yanzu dai jarumar ta ce ta samu hanyar ganawa da tauraruwar da take kauna kuma "na daure jakata ina jiran ranar da za ta ce min na hawo jirgi mu hadu da ita a koina ne kuwa a duniya. Wannan shi ne daya daga cikin manyan burikana".

Rariya

Baya ga fitowa a fina-finan da take yi, jarumar ta dauki nauyin hada fim na kanta a karon farko mai suna Rariya.

Fim din, wanda ya hada fitattun jaruman Kannywood irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Fati Washa da Maryam Booth, ya karbu sosai a wurin masu kallo.

A cewar Rahama, "Na dauki nauyin fim dinne domin na fadada ilimina a fannin fina-finai sannan na samarwa matasa karin aikin yi. Fim din yana magana ne kan irin sakacin da iyaye ke yi na rashin kula da ya'yansu da ke karatun jami'a.

Za ka ga mahaifi ya bar 'yarsa a jami'a ba tare da yana sanya mata ido ba. Wani lokaci ma 'yar ce ke ciyar da gidansu kuma babu wanda ke tambayarta inda take samun kudi.

Bayanan bidiyo,

Rahama Sadau za ta gana da Priyanka Chopra

Yawanci za ka ga Alhazan birni da lakcarori sun lalata 'yarka kafin ka ce kwabo. Kuma wannan ya samo asali ne saboda rashin kulawar iyaye. Shi ya sa na ga ya kamata a fadakar da su".

Wani abu kuma da fim din na Rariya ya fito da shi, a cewar Rahama, shi ne irin kyashi da bakin kishin da ke tsakanin mata 'yan jami'a ta yadda wata za ta iya halaka wata idan ta ga ta fi ta samun abun duniya.

Abin da ya fito fili game da rayuwar Rahama Sadau shi ne, kamar yadda ta fada, ita mace ce da ka iya shafe tsawon lokaci tana taka rawa a fina-finai da ma sauran al'amuran rayuwa, musamman ganin cewa baya ga fina-finan, tana yin wasu harkoki na wayar da kan jama'a kamar shirinta na kamfe a kan yaki da cutar daji da kuma kasuwanci.